Al'adun Gargajiya

Advertise on podcast: Al'adun Gargajiya

Categories
This podcast has
25 episodes
Language
Publisher
Explicit
No
Date created
2021/07/22
Latest episode
2026/01/27
Average duration
10 min.
Release period
11 days

Description

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

Unlock Al'adun Gargajiya podcast Email contact info,
Listeners & Audience details

Email contact information

Direct podcast contact details

Listeners

Audience numbers & engagement insights

Audience details

Podcast Insights

Podcast episodes

Check latest episodes from Al'adun Gargajiya podcast


Yadda aka gudanar da bikin addinin gargajiya na Vodun a jamhuriyar Benin 2
2026/01/27
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya kawo cigaban   yadda aka gudanar da bukukuwan addinin gargajiya na Vodun a jamhuriyyar Benin, bikin addinin gargajiya mafi muhimmanci a ƙasar.
more
Yadda aka gudanar da bikin addinin gargajiya na Vodun a jamhuriyar Benin
2026/01/20
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda aka gudanar da bukukuwan addinin gargajiya na Vodun a jamhuriyyar Benin, bikin addinin gargajiya mafi muhimmanci a ƙasar. Tun a bara ne aka ƙara wa'adin ranakun gudanar da wannan biki wanda ke samun mahalarta daga sassa daban-daban na duniya, inda ko a bara aka ga baƙi fiye da dubu 100 da suka halarci wannan biki. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more
Hausawan Turai na fuskantar barazanar ɓacewar harshe da al'adunsu
2026/01/13
Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya leƙa ne Masarautar Hausawa da ke nahiyar Turai, inda a makon Masarautar ta karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar da ya yi tattaki daga Tarayyar Najeriya, domin halartar bikin karrama Sarkin Hausawan na Turai da kuma naɗin wasu sabbin muƙaman na sarauta da suka shafi sassan nahiyar. Daya daga cikin kalubalen da Hausawa mazauna Turai ke fuskanta, shi ne bacewar harshen Hausa da al’adu a tsakaninsu, sai dai a yayin ziyarar da ya kai wa Sarkin Hausawan Turai da ke birnin Paris Alhaji Surajo Jan Kaɗo, Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar, ya yi alkawarin farfaɗo da martabar harshen na Hausa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more
Yadda aka gudanar da bikin nuna al'adu na masarautar Jiwa a Abuja
2026/01/06
Shirin Al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya yi duba game da yadda aka gudanar da bikin al'adu na masarautar Jiwa a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.......
more
Yadda aka gudanar da bikin naɗin sarautar sarkin Komadugu a Maraɗi
2025/12/02
Shirin na yau ya yada zango jihar Diffa dake Jamhuriyar Nijar,yankin da aka gudanar da bikin nadin sabon sarkin Komadugu, wanda ya samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar. Diffa dai kamar dai yadda masana tarihi suka tabbatar, ana na nufin Diwa a harshen Kanuri kenan. Kalmar ta samo asali ne daga kalmar "Di wa Nallé wa," wadda ke nuna tsabtar jiki da dai sauran abubuwan da suka shafi maza da mata na yankin. Di na nufin farin gashi, kuma Nallé na nufin lalle wanda ke da ma'ana biyu. Wannan jumla, Di wa Nallé wa, na nufin mata waɗanda, ko da a cikin tsufa, suna rina gashinsu da lalle. Tarihi ya nuna  cewa a ƙarni na 19, yankin Diffa a lokaci na karkashin masarautar Kanem-Bornu,inda a shekarar 1933 Turawan mulkin mallaka a lokacin  sun kafa yankin Komadougou, wanda aka bayyana yankin  da farko yake zaune a Bosso sannan daga baya ya koma Gueskérou. An gudanar da zaɓen sabon sarkin na komadugu a jahar Diffa a gaban hukumomin  bariki da na gargajiya da kuma sauran al’umma, wanda ya kai ga zaɓen Hassan Mamadou Abba Kyari a matsayin sabon sarkin na Komadugu. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa.
more
Yadda sana'ar sassaƙar Turmi ke fuskantar koma baya sabida ci gaban zamani
2025/11/25
Shirin "Al'adun mu na Gado" na wannan makon ya yi duba ne akan sana'ar nan ta sassaƙar Turmin, wadda ke a matsayin sana'ar al'adun gargajiya, ko da yake a yanzu samar da na'urori da ke amfanin da Turmin keyi ya mayar da sana'ar baya matuka gaya.    A baya duk macen da za'a kai gidan miji, akan hadata da Turmin babba da ƙarami kana da kuma na ƙarfe wanda za ta rika daka kayan ƙanshi wasu ma hatta Kwalli fari da ake sanyawa jarirai da shi suke dakawa, baya da kuma na da kan sakwara da kuma babba na surfe da daka.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa............
more
Yadda ƴan siyasa ke katsalandan a harkokin masarautu a Najeriya
2025/11/18
Shirin al'adun mu na gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan siyasa ke katsalandan a masarautun gargajiya a Najeriya. Danna alamar sauarre domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa
more
Bikin Kalankuwar farfaɗo da al'adun Hausawa a jihar Kano ta Najeriya
2025/11/04
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan Kalankuwar farfaɗo da al'adunmu Hausawa a jihar Kano ta arewacin Najeriya, a wani yanayi da al'umma ke fuskantar matsalar gushewar tarin al'adu a mataki daban-daban. Yayin wannan bikin Kalankuwa dai an duba fannoni daban-daban na al'adu kama daga Kiɗan gargajiya da Waƙa baya ɓangarorin wasanni da dama, bikin da ya samu halartar sarakuna da dama. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
more
Yadda al'adar ''Ƴar zaman Ɗaki'' ta zama tarihi tsakanin hausawa
2025/10/28
Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda sananniyar al'adar nan ta zaman ɗaki ke ƙoƙarin shuɗewa tsakanin al'ummar Hausawa. Shekaru aru-aru, da zarar an yi auren budurwa a ƙasar Hausa akan haɗata da ƙaramar yarinya da za ta yi mata zaman ɗaki, wanda a wasu lokutan anje kenan domin galibi aure ke raba wannan ƙaramar yarinya da gidan, kodayake wasu kan shafe wani wa'adi ne gabanin komawa gaban iyayensu na ainahi. Sai dai a ƴan shekarun nan wannan al'ada da kan yi tasiri wajen ƙarfafa zumunci ta zama tarihi, walau ko saboda yanayi na rayuwa, ko kuma saboda yadda aka tsagaita da auren ƴammata masu ƙarancin shekaru da dai sauran dalilai. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
more
Yadda aka gudanar da bikin makiyaya na Cure Salee a Jamhuriyar Nijar
2025/10/21
Shirin a wannan mako ya yi tattaki ne, zuwa ƙauyen Ingal da ke Yankin Agadez a jamhuriyyar Nijar, domin waiwayar gagarumin bikin makiyaya da ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee' wanda aka saba yi duk shekara. Bikin makiyayan na Cure Salee ya gudana ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga watan da muke ciki na Oktoba. Manufar bikin ita ce yadda za a ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya domin kafa ginshiƙin zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu. Bikin na bana ya samu halattar ƙabilun Fulani da na Abzinawa da Larabawa a Nijar ɗin da wasu daga Najeriya, da Mali da burkina Faso da kuma Aljeriya. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman...............
more
Yadda sana'ar kaɗi ke gab da gushewa tsakanin al'ummar Hausawa
2025/10/14
Shirin al'adunmu na gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya mayar da hankali ne kan gushewar sana'ar kaɗi a ƙasar Hausa duk da kasancewarta guda cikin sana'o'in Hausawan suka gada kaka da kakanni. Galibi sana'o'in Hausawa na tafiya ne da tsarin rayuwa da zamantakewar jama'a, cikin wannan kuwa har da sana'ar kaɗi wadda galibi dattawa Mata suka fi ƙwarewa akai, kodayake wannan sana'a na gab da gushewa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more
Banbanci tsakanin maita da tsafi a mahangar al'adu da addini
2025/10/07
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan mako, ya mayar da hankali kan manufar Maita da kambun baka a mahangar al'adu da kuma addini, a wani yanayi da ake yiwa wannan abubuwa biyu mabanbantan kallo. Duk da cewa wasu na yiwa waɗannan abubuwa biyu kallon abu guda, amma a wasu na kallon abubuwan biyu a matsayin mabanbanta kasancewar guda akan sameshi ne haka suddan yayinda ɗayan kuma ake iya haifar mutum da shi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more
Yadda aka bar baya da ƙura a girmamawar da ka yiwa Rarara da digirin Dakta
2025/09/23
Shirin Al’adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la’akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen. Tun cikin makon jiya masana da sauran jama’ar gari ke tofa albarkacin bakunansu akan karramawar  da wata Jami’a mai suna European-American University ta yi wa fitaccen mawaƙin siyasa a Najeriya Dauda Kahutu Rarara, wanda ta bai wa Digirin Girmamawa na Dakta. Reshen Jami’ar da bayanai a yanar gizo suka nuna cewar hedikwatarta na ƙasar Faransa ne ta yi bikin Karrama mawaƙi Raran ne a Abuja, ranar Asabar, 20 ga watan nan na Satumba, taron da ya samu halartar wasu fitattun mutane. Sai dai Kash! ‘yan sa’o’i bayan bikin da aka yi Jami’ar da ake alaƙanta da Turai da Amurka ta ce ba ta fa san zance ba, domin ba da yawunta aka miƙa wa fitaccen mawaƙin siyasar Digirin na Girmamawa ba, zalika dukkanin mutanen da suka yi iƙirarin alaƙanta kansu da ita ta barranta da su, domin sun yaudari mutane ne da sunanta domin samun damar karɓar na goro a huce. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more
Sannu a hankali sana'ar ƙira na shuɗewa a jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar
2025/09/16
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda sannu a hankali sana'ar kira ke shudwa musamman ta ƴan Kabilar Abzinawa da ke jihar Agadez a jamhuriyar Nijar. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Issa.
more
Bikin cika shekaru 10 da fara Ranar Hausa ta Duniya - kashi na biyu
2025/09/02
Shirin Al’adunmu na Gado a wannan makon ya ɗora ne akan Bikin ranar Hausa ta Duniya, bikin da yake mayar da hankali wajen bunƙasawa da faɗaɗa harshe da kuma al’adun Hausawa a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar 2015 aka fara gudanar da wannan biki na ranar Hausa ta Duniya a Najeriya da sauran ƙasashen da ke da al’ummar Hausawa, bikin da sannu a hankali ya riƙa samun karɓuwa gami da faɗaɗa har zuwa wannan lokaci da ya shafe shekaru 10 cif.
more

Podcast reviews

Read Al'adun Gargajiya podcast reviews


0 out of 5
0 reviews

Podcast sponsorship advertising

Start advertising on Al'adun Gargajiya & sponsor relevant audience podcasts


What do you want to promote?

Ad Format

Campaign Budget

Business Details