1577791862
Ilimi Hasken Rayuwa

Advertise on podcast: Ilimi Hasken Rayuwa

Categories
This podcast has
24 episodes
Explicit
No
Date created
2021/07/22
Latest episode
2026/09/29
Average duration
10 min.
Release period
11 days

Description

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’Adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.

Podcast episodes

Check latest episodes from Ilimi Hasken Rayuwa podcast


Jigawa ta gabatar da tsarin rage barace-baracen Almajirai a jihar
2026/09/29
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan daɗaɗɗen batun nan na yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya matsalar da har kawo yanzu ta ƙi ci taki cinyewa. Wani Rahoton UNICEF ya bayyana jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a matsayin jihohin da ke da rinjayen yaren da basa zuwa Makaranta, inda a jumlace ƙasar ta yammacin Afrika ke da yara fiye da miliyan 18 da basa zuwa Makaranta, galibinsu a arewacin ƙasar. Tuni Jihar Jigawa ta ɗaura ɗamarar yaƙi da wannan matsala, inda ta gabatar da wani sabon tsarin mayar da ɗimbin yara makarantu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Gwamnatin Kano na shirin tilasta koyar da ilimin Kwamfuta a makarantun Firamare da Sakandare
2026/09/22
Shirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda majalisar dokoki jihar Kano ta bukaci a mayar da ilimin Kyamfuta dole a matakin makarantun Firamare da Sakandare. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Gwamanatin Najeriya na shirin Horas da malamai sama da miliyan guda
2026/09/15
A yau shirin ya mayar da hankali ne kan matakin gwamnatin Najeriya kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka da ke shirin horas da malaman makaranta sama da miliyan guda. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Gudunmowa ko kuma illar da shafukan sada zumunta ke yiwa al'adun Bahaushe
2026/09/01
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya duba irin yadda guguwar kafafen yada labarai da shafukan Internet ke barazana ga al'adun Hausawa da salon rayuwarsu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Yadda matasa suka ƙera jirgi maras matuƙi mai cin Kilomita 30 a Kano
2026/08/18
Shirin a wannan makon ya leka Kanon Najeriya, inda aka gano wani sabon tarihin bunkasar kimiyya da fasaha da matasan yankin ke jagoranta. Wannan gagarumar bajinta dai wani matashi Abubakar Waiya, wanda ya daɗe yana fafutukar kera na'urorin shawagi ne ya ƙera jirgi maras matuƙi domin taimakawa ɓangaren tsaro da kuma boma. Jirgin da ya kera a yanzu yana da ikon tashi da kansa har na tsawon kilomita 30 ba tare da ya ɓace ba. Wannan na'ura tana da aiyuka na musamman da aka tsara ta don yi, kamar feshin maganin ƙwari a gonaki na zamani da kuma kai magungunan gaggawa zuwa yankunan karkara da motoci ba su iya zuwa saboda rashin hanya. Duk da wannan gagarumar nasara, babban ƙalubalen da ke gaban matasan shi ne tsarin dokoki na ƙasa. Masu fafutuka na ganin cewa, idan har gwamnati da masu ruwa da tsaki suka ba wa waɗannan matasa dama da goyon baya, wannan ƙoƙari daga birnin Kano zai zama tushen samar da dabarun tsaro da aikin gona na zamani ga ɗaukacin yammacin Afirka. Tambayar da ta rage anan ita ce: Shin gwamnati za ta tallafa wa wannan fasaha ta gida don ta bunkasa, ko kuwa za a zura ido ta ɓace ne?
Makomar ilimin yara a Kano na cikin halin rashin tabbas
2026/07/14
Shirin na wannan makon cigaba ne kan wanda muka gabatar a makon jiya, wanda ya gano yadda yara a wasu yankunan jihar Kano basa zuwa makaranta saboda yawon tallace-tallace domin tara kudin kayan ɗaki. Yayin da su kuma mazan suke diban yashi da fasa Dutse, da sunan wai su taso suna da sana'ar dogaro da kai. Yankunan da wannan lamari yafi kamari sun hada da Challawa, Kafin Maiyaki, Madobi, Gora, da Kanwa. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata mun kawo rahoton yadda wasu makarantu suka koma dandalin shaye-shaye a garin Meshumi dake karamar hukumar Ungogo.
Yadda makomar ilimin yaran karkara a Najeriya ke cikin rashin tabbas
2026/07/08
A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai. A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sabon rahoton hukumar UNICEF ya nuna cewa, jihohin Kano, Katsina, da Jigawa ne ke kan gaba a faɗin Najeriya wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inda a faɗin kasar kuwa, akwai yara sama da miliyan goma sha takwas da dubu ɗari uku da makoma ta iliminsu ke cikin haɗari. Sau da yawa, wannan zargi na komawa ga gwamnati, sai dai abin tambayar shine, shin ko laifin na iyaye ne da al'umma, ko kuwa suma hukumomi akwai nasu kason? Mun ziyarci garin Meshumi da ke karamar hukumar Ungoggo a jihar Kano, inda shirin ya tarar makarantar firamare na nan a gine, amma dakin karatu ya zama kufai. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Shamsiyya Haruna
Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya
2026/06/30
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya. Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa. Wannan littafi, kamar yadda masana da dama suka bayyana, ya zo ne a daidai lokacin da matasan yanzu ke ƙara nisanta da asalin tarihinsu. To ko me ya sa mawallafin, Kabiru Ahmad Kwalli,  ya ɗauki tsawon lokaci yana wannan bincike? Ga abinda ya shaida mana lokacin da muke zantawa da shi.
Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos
2026/06/23
A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni. Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin New York, an dawo da shi gida Afirka domin tattauna ainihin matsaloli da ci gaban nahiyar ke fuskanta, kuma a bana, fiye da rukunonin tattaunawa 340 ne aka shirya, inda aka haɗa masana daga sassan duniya. Shekarar 2026 ta yi daidai da cikar kungiyar LSA shekaru 10 da kafuwa, inda aka gudanar da taron ƙarƙashin taken makomar ilimin nahiyar Afirka a wannan ƙarni. Wani sashe mai muhimmanci a taron shi ne tattaunawa kan littafi na musamman mai suna 'Our Digital Lives and Indigenous Pathways', wanda masana suka duba yadda za a haɗa fasahar zamani da dabarun gargajiya na Afirka don samun ci gaba mai dorewa. Baya ga tattaunawar kimiyya, taron ya haɗa da baje kolin fasaha na musamman mai taken 'Histories on Scissors: The Black Essence on the Map of Being' wanda Dominic James Aboi daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya gabatar. An kuma tattauna makaloli kan addini da rashin addini a Arewacin Najeriya. An dai gudanar da wannan taro ne domin nazarin al'adun zamani da na gargajiya, inda masana suka gabatar da maƙaloli kan tarihin Afirka, al'adu, da kafafen yaɗa labarai haɗi da baje kolin dabarun bincike na zamani. A taron na bana, masana sun gano muhimman abubuwa da suka shafi makomar nahiyar Afirka ta fuskar ilimi, zamantakewa, da fasaha, kuma babban jigon da aka mayar da hankali akai shi ne yadda za a fassara binciken ilimi ya zama abin da zai amfani rayuwar al'umma kai-tsaye. Haka zalika an gano cewa ko da yake yawan binciken da masana da ke zaune a cikin Afirka ke fitarwa ya ƙaru sosai, amma ingancinsa da kuma bayyanarsa a manyan jaridun ilimi na duniya ya ragu sosai.
Yadda talauci ke hana ɗalibai cikar burinsu
2026/06/09
Shirin Ilimi hasken rayuwa na wanna Mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsin tattalin arziki ke tilstawa ɗalibai haƙura da cikar burinsu na karatu, don kawai neman abin kaiwa baka, a kowacce rana. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsioyya Haruna.
Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa
2026/06/02
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya sake waiwayar matsalar nan ce ta yawaitar yaran da ba za zuwa makaranta a arewacin Najeriya, batun da a fannin ilimi ke ci wa al’ummar yankin tuwo a ƙwarya.  Masu iya magana dai na cewa ‘mai rai ba ya rasa motsi’ domin kuwa duk da girman da wannan matsala ta yi a Najeriya musamman ma yankin arewacin ƙasar, akwai waɗanda suka tashi tsaye wajen ganin sun kawo ƙarshen wannan ƙalubale, kuma har ma an fara samun sakamako kyakkyawa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman................
Ɗimbin matasa na haƙura da karatun boko saboda rashin tabbas kan samun aiki
2026/05/19
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matasa a baya-bayan na ke haƙura da ilimin boko saboda shakku kan yiwuwar samun aikin yi. Matsalar rashin aikin yi bayan shafe tsawon shekaru ana karatu tare da kashe maƙuden kuɗaɗe ya sanya matasa da dama musamman waɗanda ba ƴaƴan wasu ba ajje tunanin karatu tare da mayar da hankali a kasuwanci da koyon sana'a saboda abin da suka kira rashin tabbas na cin moriyar karatun da suka yi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya
2026/05/12
A yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya. Gwamnatin ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai hanyar neman ilimi da kuma ƙarfafa musu gwiwa ta fuskar kuɗi. Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya sanar da cewa ɗaliban da ke son shiga Kwalejin Ilimi yanzu ba sai sun rubuta jarrabawar UTME ba. Amma dole ne ɗalibi ya kasance yana da aƙalla darussa biyar a sakamakonsa na sakandare. Duk da cewa ɗalibi ba zai rubuta jarrabawa ba, dole ne ya yi rajista da hukumar JAMB don tantance takardunsa domin samun gurbin karatu ta tsarin CAPS. Bayan rage wa ɗalibai wahalar jarrabawa, gwamnatin ta kuma samar da tallafin karatu domin jawo hankalin kwararru zuwa fannin koyarwa. inda ta amince da biyan ɗaliban da ke karatu a kwalejojin ilimi na gwamnati alawus din naira naira 50,000 a kowane zango, waɗanda ke karatun digiri a fannin ilimi a jami’o’in gwamnati za su samu naira naira 75,000 Masana a fannin ilimi dai na ganin cewa, wannan wata babbar dama ce ga iyaye da ɗalibai da ya kamata su yi amfani da ita don sauƙaƙa wa kansu nauyin kuɗi da kuma samun gurbin karatu cikin sauƙi. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shrin
Tasirin fasahar zamani wajen bunƙasuwar aikin jarida
2026/05/05
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin ranar ƴancin ƴan Jaridu ta duniya da ke gudana a kowacce ranar 3 ga watan Mayu, bikin da ke zuwa a wannan karon cikin wani yanayi da aikin na Jarida ke ganin koma baya. Akwai dai ƙorafe-ƙorafe daga sassa daban-daban kan yadda aikin  na Jarida ke fuskantar barazana kodayake masu ruwa da tsaki a wannan fanni sun ce yanayin yaɗa labaran ya samu ci gaba da matuƙa ta sakamakon yaɗuwar fasahar zamani. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Yadda makarantun tsangaya suka fara gauraya karatun addini da na Boko don tafiya da zamani
2026/04/28
Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda makarantun tsangaya da na Islamiyya suka fara gauraya karatun addini da na zamani a ƙoƙarin da suke yi na tafiya da zamani da kuma amun tallafi daga gwamnatoci da manyan ƙungiyoyi na duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

Podcast reviews

Read Ilimi Hasken Rayuwa podcast reviews


0 out of 5
0 reviews

Podcast sponsorship advertising

Start advertising on Ilimi Hasken Rayuwa relevant audience podcasts


What do you want to promote?

You may also like to advertise on these Podcasts