Lafiya Jari ce

Advertise on podcast: Lafiya Jari ce

Categories
This podcast has
24 episodes
Language
Publisher
Explicit
No
Date created
2021/07/22
Latest episode
2026/02/02
Average duration
11 min.
Release period
9 days

Description

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.

Unlock Lafiya Jari ce podcast Email contact info,
Listeners & Audience details

Email contact information

Direct podcast contact details

Listeners

Audience numbers & engagement insights

Audience details

Podcast Insights

Podcast episodes

Check latest episodes from Lafiya Jari ce podcast


Najeriya ta ƙaddamar da dokar ta ɓaci a harkar kiwon lafiya
2026/02/02
A wannan makon shirin zai yi dubi ne kan dokar ta baci a harkan lafiya da gwamnatin Najeriya ta kaddamar inda ta sanar da karuwar cutuka masu alaka da gurbatacciyar iskar da jama’ar ƙasar ke shaka. Hukumar duba gari ta Najeriya ko kuma Environmental Health Council a Turance ita ta sanar da wannan dokar ta baci inda tace munin cutukan dake alaka da numfashi da kuma cutar kansa dake karuwa yasa dole gwamnati da dauki tsauraran matakan, kamar yadda shugaban hukumar Dr Yakubu Muhammad Baba ke cewa. Gurbacewar iska a muhallin ɗan adam kan faru ta hanyoyi da dama kama daga yawaitar hayaƙin da motoci ke fitarwa da kone-konen dazuka ko ƙona itace a gidajen jama’a dama masana’antu da kan fitar da tiriri mai guba, wanda kuma kai tsaye ke cutar da lafiyar ɗan adam tare da haddasa cutuka ko ta’azzarar lalura masu fama da cutukan lumfashi, lamarin da ƙwararren likita Dr Lawal Musa Tahir ke cewa illar gurɓatacciyar iska ta wuce duk inda ake tunani. Ku latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu........
more
An fara gangamin rigakafin cutar Typhoid irinsa na farko a Jamhuriyyar Nijar
2026/01/19
Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan gangamin rigakafin cutar Typhoid da mahukuntan Jamhuriyyar Nijar suka faro a faɗin ƙasar, irinsa na farko da aka taɓa gani a tarihi a wani yanayi da ake ganin ta’azzarar wannan cuta a ƙasar ta yankin Sahel. Wasu alƙaluman hukumar Lafiyar Jamhuriyyar Nijar a 2021 sun ce mutane dubu 30 suka kamu da cutar, a wancan lokaci wadda ta haddasa mutuwar mutane 400. Kodayake a baya-bayan nan babu cikakkun alƙaluman ta’adin cutar, sai dai matakin mahukuntan na fara wannan rigakafi ya nuna tabbacin ta’azzararta. Jihar Agadez na ɗaya daga cikin yankunan da cutar Typhoid ta fi yaɗuwa, kuma tuni aka faro wannan rigakafi da zai shafi mutanen da shekarunsu ya fara daga 1 har zuwa 19 a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.............
more
Illolin da sauyin yanayi ke haifarwa ga lafiyar jama'a
2026/01/12
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali ne kan illolin da sauyawar yanayi ke haifarwa ga lafiyar jama’a, musamman ganin yadda hunturu ya fara amma kuma kwatsam ya ɗauke cikin ƙanƙanin lokaci tare da shigowar zahi, lamarin da ya haddasa cutuka masu yawa a tsakanin jama’a.
more
Ɓullar annobar ƙyanda ta t'azzara a sassan Najeriya
2026/01/05
A wannan makon shirin tare da Azima Bashir Aminu  ya mayar da hankali kan fitar wasu sabbin alƙaluman hukumar NCDC masu tayar da hankali matuƙa da ke nuna yawaitar ɓullar cutar ƙyanda ko kuma baƙon dauro dama ƙaruwar mutanen da take kashewa a sassan Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.......
more
Illar ta'ammali da magungunan ƙara kuzari ko rage gajiya da jama'a ke yi
2025/12/22
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan karon ya mayar da hankali kan yadda ɗabi’ar ta’ammali da wasu nau’ikan tsumin gargajiya da sunan samun kuzari ko kuma ƙarfin jiki ke ci gaba da ta'azzara tsakanin jama'a, wanda masana suka yi ittifaƙin na da matuƙar illa ga lafiyar jama’a. Tsumi na baya-bayan nan da ke samun karɓuwa tsakanin jama’a musamman masu ayyukan ƙarfi shi ne ‘’Wankin ciki’’ ko kuma Gyaran Gida ko kuma Aji Garau kamar yadda wasu ke kiranshi, tsumin da ke ɗauke da magungunan gargajiya, kuma ya ke ci gaba da samun karɓuwa tsakanin dukkanin rukunin mutane kama daga matasa da kuma magidanta. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more
Dabarun yaƙi da ƙibar da ta wuce ƙima ko kuma Obesity tsakanin matasa
2025/12/15
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir a wannan mako ya mayar da hankali kan wasu alƙaluman mujallar Lancet da ke nuna cewa nan da shekarar 2050 fiye da kashi 50 na yawan al’ummar Afrika musamman Afrika za su zama masu ƙibar da ta wuce ƙima ko kuma Obesity a turance. Alƙaluman na Lancet wanda aka tattara bayan gwaji a ƙasashe fiye da 50 ya nuna cewa matsloli masu alaƙa da cimaka da kuma rashin motsa jiki su ke matsayin kan gaba da za su haddasa wannan matsala ta Obesity ko kuma ƙibar da ta wuce ƙima. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more
Bincike ya gano cewa kashi 38 na matan Damagaram ne kaɗai ke haihuwa a asibiti
2025/12/08
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali game da yadda wasu mata a Jamhuriyyar Nijar ke ƙin amincewa da haihuwa a asibiti duk kuwa da haɗarin da ke tattare da haihuwa a gida. Wasu alƙaluman baya-bayan nan da mahukuntan jihar Damagaram suka tattara, ya nuna cewa ƙasa da kashi 40 na mata ne ke haihuwa a asibiti duk kuwa da yadda mahukunta suka mayar da haihuwar kyauta a asibitocin jihar waɗanda aka samar da su a gab da jama'a. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more
Kamaru ta yi nasarar rage mutuwar mata yayin haihuwa a cikin shekaru 4
2025/12/01
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan wasu alƙaluma da ke nuna cewa cikin shekaru 4 da suka gabata Kamaru ta yi nasarar rage yawan matan da ke mutuwa a lokacin haihuwa ko kuma goyon ciki. Alƙaluman hukumar kula da lafiyar yara da na DHS mai tattara alƙaluman jama’a sun nuna da cewa da kusan rabi ne aka samu raguwar mace-macen matan, inda daga mace-macen mata dubu 2 cikin dubu 100 a 2018 adadin a yanzu ya dawo mace-macen mata 406 cikin dubu 100 duk shekara wanda ke nufin gagarumar nasara, kodayake ministan lafiya na ƙasar Manaouda Malachie ya ce sun yi amfani da wasu tsare-tsare gabanin samun wannan nasara.
more
Fahimtar ƙwararru game da tasirin Hamma ga lafiyar ɗan adam
2025/11/24
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir a wannan makon ya mayar da hankali kan wasu daga cikin ɗabi’un jikin ɗan adam da kan faru ba tare da shiri ba, cikin waɗannan ɗabi’u kuwa har da hamma, inda shirin zai duba tasirinta ga lafiyar ɗan adam. Rubuce-rubucen masana game da ɗabi’ar ta hamma na alaƙanta ta da barci ko gajiya ko kuma yunwa, sai dai fa masanan sun kuma bayyana cewa Hammar na taka muhimmiyar rawa a tsarin lumfashin ɗan adam, musamman ta fuskar daidaita yawan iskar da mutum ke shaƙa wato Oxygen da kuma wadda ya ke fitarwa wato Carbon dioxide. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more
Yadda cutar Suga ke mamaya a ƙasashen Afrika
2025/11/17
Shirin lafiya jari ce na wannan mao ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da ke cewa mutane akalla miliyan 24 ne ke fama da cutar Suga a Nahiyar Afrika kawai. Wannan kuwa na faruwa ne a dai-dai lokacin da cutar ke sauya salo da tsanani ga masu fama da ita, baya ga bijirewa magani.   Danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
more
Mutane fiye da dubu 28 na mutuwa duk shekara saboda gurɓacewar iska a Ghana
2025/11/10
A wannan makon shirin Lafiya jari ce ya mayar da hankali kan wani bincike a Ghana da ke nuna yadda mutane sama da dubu 28 ke mutuwa duk shekara saboda gurbacewar iska. Alƙaluman hukumar kula da Lafiya ta Ghana ne ke sanar da wannan adadi, wanda kai tsaye ke nufin duk mintuna 19 wannan matsala ta gurɓatacciyar iska kan sabbaba mutuwar mutum guda a wannan ƙasa ta yammacin Afrika, batun da ke buƙatar kulawar gaggawa don ɗaukar matakan da suka dace. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...
more
Akwai alaƙar mai ƙarfi tsakanin cutar yunwa da taɓuwar ƙwaƙwalwa
2025/10/27
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya mayar da hankali kan alaƙar cutar yunwa da kuma lafiyar ƙwaƙwalwa, inda a cikin shirin zakuji yadda masana a ɓangaren suka alakantawa waɗannan matsaloli biyu a matsayin lalurori masu tafiya kafaɗa da kafaɗa da juna. A kowacce ranar 10 ga watan Oktoba ne duniya ke gudanar da gangamin kula lafiyar ƙwaƙwalwa don bikin ranar ta lafiya ƙwaƙalwa ko kuma World Mental Health Day a turance, da nufin wayar da kai game da muhimmancin lafiyar ƙwaƙwalwa dama matsalolin da ka iya barazana ga ƙwaƙalwa, sai dai a wannan karon ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa ta MSF ta alaƙanta ƙarancin abincin mai gina jiki da ke haddasa cutar da yunwa da matsalar ƙwaƙwalwa...... wannan shi ne maudu’in da shirin Lafiya Jari ce na wannan mako zai mayar da hankali akai, sai ku biyo mu.... Wani rahoto da MSF ta fitar a ranar ta 10 ga wata ta koka da ƙaruwar yaran da ke fama da cutar yunwa sakamakon ƙarancin abinci mai gina jiki, wanda ta ce matsala ce kai tsaye da ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwa. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
more
An gudanar da gangamin wayar da kai akan cutar daji a Jamhuriyar Nijar
2025/10/20
Kowanne watan Oktoba, lokaci ne da ɓangarorin lafiya a Jamhuriyyar Nijar ke amfani da shi wajen gudanar da gangamin wayar da kai a ƙasa baki ɗaya game da cutar sankara ko kuma Cancer wadda ake ganin ƙaruwar masu kamuwa da ita a sassan wannan ƙasa ta yankin Sahel,,,, wannan shi ne maudu’in da shirin na Lafiya jari ce zai mayar da hankali akai sai ku biyomu. Jamhuriyyar Nijar na ganin sabbin kamuwa da cutar ta cancer dubu 9 da 787 duk shekara ciki kuwa har da mata masu kamuwa sankarar mama dubu 2, wanda ke matsayin wani ɓangare na jumullar mata miliyan 2 da dubu 300 da ke kamuwa da sanakarar maman duk shekara a sassan duniya bisa alƙaluman hukumar WHO.
more
Yadda Cholera ta kashe mutane kusan dubu 5 a sassan Najeriya cikin shekaru 5
2025/10/13
Shirin a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan yawaitar samun cutar Kwalara ko kuma amai da gudawa  a sassan Najeriya, cutar da a baya-bayan nan ta kashe ɗimbin al'umma a ƙasar mafi yawan jama'a a Nahiyar Afrika. Wasu alƙaluma da hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasar NCDC ta fitar sun nuna cewa mutane kimanin dubu biyar (5,000) cutar ta kwalara ta halaka a sassan Najeriyar daga shekarar 2020 zuwa 2025 da muke ciki. Latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Aminu.............
more
Cutar Hanta ta Hepatitis nau'in B na yaɗuwa kamar wutar daji a Najeriya
2025/10/06
Shirin a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan ciwon hanta nau’in B ko kuma Hepatitis B a turanci, cutar da masana ke gargaɗi game da yadda ta ke yaɗuwa kamar wutar daji tsakanin jama’a. Wasu alƙaluma sun nuna yadda ake da mutum fiye da miliyan 257 da ke fama da wannan cutar, a wani yanayi da Najeriya ke sahun ƙasashe 5 masu ɗauke da kashi 60 na masu wannan cuta a duniya baki ɗaya. Masana a ɓangaren lafiyar Najeriya sun bayyana yadda wannan cuta ta Hepatitis B ke yaɗuwa kamar wutar daji a sassan ƙasar, kuma abin dubawar shi ne yadda mutane da yawa ke rayuwa da cutar yanzu haka ba tare da sanin suna ɗauke da ita ba, kan hakan kuma muka nemi ji daga masana irin Dr Misbahu Sahabi na Cibiyar Kiwon Lafiya ta tarayya da ke garin Birnin Kudun jihar Jigawa, wanda ke cewa tun farko cutar na da rabe-rabe wato mai haɗari da kuma mai sassaucin illa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more

Podcast reviews

Read Lafiya Jari ce podcast reviews


0 out of 5
0 reviews

Podcast sponsorship advertising

Start advertising on Lafiya Jari ce & sponsor relevant audience podcasts


What do you want to promote?

Ad Format

Campaign Budget

Business Details