
Advertise on podcast: Tambaya da Amsa
This podcast has
24 episodes
Language
EnglishPublisher
RFI HausaExplicit
No
Date created
2021/07/22
Latest episode
2026/01/31
Average duration
21 min.
Release period
10 days
Description
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.
Unlock Tambaya da Amsa podcast Email contact info,
Listeners & Audience details
Email contact information
Direct podcast contact details

Listeners
Audience numbers & engagement insights

Audience details
Podcast Insights

Podcast episodes
Check latest episodes from Tambaya da Amsa podcast
Tasirin taron tattalin arziki na Davos da ya gudana a Switzerland
2026/01/31
A cikin shirin Tambaya da Amsa daga sashen hausa na RFI,a yau shirin zai dora ne a cigaban tattaunawa a kan tasirin taron Davos wadda aka saba shekara-shekara kan duba lamuran tattalin arzikin duniya.
Ga ci gaban tattaunawa tare da Dr. Kasim Garba Kurfi masanin tattalin arziki na ƙasa da ƙasa dake tarayyar Najeriya.
Menene yake haifar da sukar ciki ko kuma naɗewar hanji a cikin ɗan Adam
2026/01/24
Shirin tambaya da amsa na wannan mako zai fara ne da bayani akan abinda ke haifar da sukar ciki ko kuma naɗewar hanji a cikin mutum.
Sai kuma tambayar da ke neman ƙarin bayani a kan yaushe aka fara taron duba lamuran tattalin arziki na Duniya da ake kira Davos world economic forum kuma wane tasiri yake da shi ga duniya da kuma yankin mu na Afirka.
Sai kuma tambayarmu ta gaba wadda ke buƙatar ƙarin haske kan irin gudunmawar da ake la’akari da su kafin a ba wa mutum kyautar lambar yabon zaman lafiya ta duniya wato Nobel peace price, kamar yadda aka baiwa ƴar ƙasar Venezuela Maria Corina Machado.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin
Me ya sa darajar kuɗaɗen wasu ƙasashen larabawa su ka fi na Amurka daraja?
2026/01/17
Shirin tambaya da amsa da ke zuwa muku da wasu amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu su ka aiko mana, mu kan mika wadanan tambayoyi ga masana domin baku amsar da ta dace................
Tambaya da amsa: Ko ta yaya ake gane ƙarfin tattalin arziƙin ƙasa?
2026/01/10
Shirin Tambaya da amsa tare da Nasiru Sani a wannan makon ma bai yi ƙasa a gwiwa ba, inda ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana kamar yadda aka saba.
A cikin shirin za ku ji amsar tambaya kan irin hikimomin da ake amfani dasu dasu ne wajen gane Bunkasar tattalin arzikin ƙasa.
Sai kuma amsa kan wannan tambaya da ke cewa: ko me ke haddasa kamuwa da cutar Amosanin Makogwaro wato Strep throat infection kuma mene ne alamunta?
Ku latsa alamar sauti don jin amsar waɗannan dama wasu ƙrin tambayoyin da aka tattauna akansu cikin shirin.
Ko shan magani na yiwa ɗan Adam illa ?
2026/01/03
A cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako daga sashen hausa na Rfi,shin ko gaskiya ne duk magani da mutum ya sha ya na da tasa illar da zai masa?
Nasiru Sani ya tunttubi masana a kai.....
Tarihin kafuwar kungiyar SASSAKAWA foundation
2025/12/20
Tarihin kafuwar kungiyar SASSAKAWA foundation dake taimakawa a harkar manoma a Najeriya, wai shin da gaske ne kungiyar daga Japan aka kafata kuma wanene ya kafata?
Akan wannan tambaya ce muka zanta da Dr Abdulhamid Gambo mataimakin shugaban SASSAKAWA Foundation a Najeriya.
Tambaya da Amsa: Taƙaitaccen tarihin Marigayi Sheikh Ɗahiru Bauchi
2025/12/06
Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani, bisa al'ada kan amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko, inda a yau guda cikin tambayoyin da wannan shiri ya amsa shi ne buƙatar taƙaitacce tarihin fitaccen Malamin Islaman nan a Najeriya kuma jigo a Dariƙar Tijjaniya, shehu Usman Dahiru Bauchi wanda Allah ya yiwa rauswa a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da muke ta 2025 .
Don samun amsar wannan tambaya ce wakilin RFI a jihar Bauchin Najeriya Ibrahim Malam Goje ya zanta da Dr Fathi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, daya daga cikin 'ya'yan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, kuma daya daga cikin wadanda suka taɓa rubuta littafi a kan marigayin.
Ku latsa alamar ƙari don jin amsar wannan tambaya da sauran tambayoyin da ke ƙunshe cikin wannan shiri tare da Nasiru Sani.
Tarihin shahararren jarumin fina-finan indiannan Dharmendra
2025/11/29
Shirin tambaya da amsa na wannan mako ya mayar da hanakali ne a kan tarihin shahararren jarumin fina-finan indiannan wato Dharmendra wanda ya rasu a ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar 2025.
Abubuwan dake haddasa cutar toshewar hanyoyin numfashi wato Asthma
2025/11/22
Shirin Tambaya da Amsa na wannan mako, zai fara ne da bayani dangane da abubuwan dake haddasa cutar toshewar hanyoyin shaƙar numfashi wato Asthma a turance.
Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Nasiru Sani....
Abubuwan da ke haddasa warin baki da kuma hanyoyin magance matsalar
2025/10/18
Shirin tambaya da amsa na wannan mako tare da Nasiru Sani, ya amsara tambaya akan abinda ke haddasa warin baki da kuma hanyoyin da ya kamata abi wajen magance matsalar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Nasiru Sani...............
Ƙarin bayani akan adadin Nahiyoyin duniya da kuma wacce ce ta fi faɗin ƙasa
2025/10/11
Shirin tambaya da amsa na wannan mako tare da Nasiru Sani, ya amsa tambayoyin da ke neman karin bayani akan inda tsakiyar Najeriya ya kasance, da tambayar da ke neman sanin Nahiyoyi nawa ne a duniya kuma wacce ce ta fi faɗin ƙasa sannan wacce ta fi yawan mutane? da kuma tambayar da ke cewa, don Allah ku tambaya mana masana tattalin arziki akan mece ce TIN number kuma ina ake samunta sannan mene ne aikinta a Najeriya?
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.............
Cigaban bayani bayani akan kafa sabuwar rundunar sojin ko-ta-kwana ta ECOWAS
2025/10/04
A yau shirin tamabaya da amsa zai fara ne da cigaban amsar tambayar dake neman karin bayani akan sabuwar rundunar sijin ko-ta-kwana wadda ƙungiyar ECOWAS ke shirin kafawa, da kuma cigaban amsar tambayar da aka yi game da cutar daji mafitsara... Wanna da ma wasu tambayoyin ne za mu amsa a cikin shirin 'Tambaya Da Amsa na wannan makon.
Ƙarin bayani akan kafa sabuwar rundunar sojin ko-ta-kwana ta ECOWAS
2025/09/27
A yau shirin tamabaya da amsa zai fara ne da tambayar dake neman karin bayani akan sabuwar rundunar sijin ko-ta-kwana wadda ƙungiyar ECOWAS ke shirin kafawa.. Wanna da ma wasu tambayoyin ne za mu amsa a cikin shirin 'Tambaya Da Amsa na wannan makon.
Harajin kashi 5 da gwamnatin Najeriya ke son ƙarawa akan kuɗin man fetur
2025/09/20
Ko menene harajin kashi 5 da gwamnatin Najeriya ke son ƙarawa akan kuɗin man fetur ga duk mai bukata?, Ku tambaya mana masana harkokin tsaro domin su yi mana bayani akan mene ne ma'anar ƴansandan jihohi da ake ta muhawara a kai a Najeriya, kuma shin yin hakan zai haifar da ɗa mai ido? wasu cikin tambayoyin masu sauraro kenan da shirin Tambaya da Amsa na wannan mako ke ɗauke da amsoshinsu tare da Nasiru Sani....
Latsa alamar sauti don sauraren shirin........
Gaskiyar lamari dangane ayoyin tambayar da ake ɗigawa kan Ingantaccen Iri
2025/09/13
A cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako tare da Nasiru Sani, masana sun amsa tambayoyi game da abubuwan da ke tsaida wa Mata haihuwa da Sahihancin Ingantaccen Iri da ake samarwa wato GMO a turance, sai kuma illar da gyatsar magwas ke ita ga mai yin ta.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin........
Podcast reviews
Read Tambaya da Amsa podcast reviews
Podcast sponsorship advertising
Start advertising on Tambaya da Amsa relevant audience podcasts
You may also like to advertise on these Podcasts

4.4371061566
The Megyn Kelly Show
SiriusXM

4.888901269
Fearless with Jason Whitlock
Blaze Podcast Network

4.8118931000
Mind Pump: Raw Fitness Truth
Sal Di Stefano, Adam Schafer, Justin Andrews, Doug Egge

4.8102131585
Tara Brach
Tara Brach

4.541561215
Something You Should Know
Mike Carruthers | OmniCast Media

4.513841343
Strictly Anonymous Confessions
Kathy Kay

4.8292781897
Fantasy Footballers - Fantasy Football Podcast
Fantasy Football

4.62382612
Football Weekly
The Guardian

4.45387666
Two Judgey Girls
Two Judgey Girls

3.8258501152
The Viall Files
Nick Viall