
Advertise on podcast: Hausa Fatwa
This podcast has
30 episodes
Publisher
IlmQSExplicit
No
Date created
2026/04/14
Latest episode
2026/10/04
Average duration
55 min.
Release period
8 days
Description
Islamic lectures in Hausa language from from world renowned scholars.
Podcast episodes
Check latest episodes from Hausa Fatwa podcast
Fatawowin Rahama: Q&A 27-09-2026 - Prof. Sani R/Lemo
2026/10/04
Fatawoyin Rahma
Ranar Lahadi 16/4/1446- 27/9/2026
Tambayoyi da Amsoshi tare da _Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON_
1. Hukuncin ba da umurni ( prompt) ga Artificial Intelligence (“AI”) ya sa hotuna mutane suna aiwatar da umurnin da ake so su aiwatar!
2. Hukuncin cin allowance da ake bawa mai Hidimar ƙasa (NYSC) da ba ya zuwa wajen aikin da aka sa shi yayi (primary assignment).
3. Hukuncin yin Sallah a massallacin da ba a kiran Sallah!
4. Ya hallata mutum ya kar6i bashin da Moniepoint suke bayarwa!
5. Ana iya taya mai azumin kaffara in ya gaji?
6. Maganin Kambun Baka!
7. Hukuncin shan Maganin ƙarfe (Tauri)
8. Tsawon wanne Lokaci ne mutum zai zauna ba tare da iyalansa ba!
9. Hukuncin Sallah da gajeran wando!
10. Hukuncin wanda in ya ta shi neman aure a ce masa ga irin sunan matar da zai aura bisa ilimin taurari!
11. Akwai hadisin da ya ce mace mai aure tafiyarta daga daki zuwa kitchen ta na da ladan umrah ?
12. Hukuncin sana’ar siyar da karnuka?
13. Hukuncin mamu da yayi dariya ana tsaka da Sallah!
14. Hukuncin gyara ƙabarin wanda ba musulmi ba!
15. Akwai hadisi da Annabi ﷺ ya ambaci mutane dubu 70 da za su shiga aljanna ba tare da hisabi ba?
16. Akwai fifiko tsakanin sahun gaba a Sallah da sahun baya?
17. Hukuncin wanda yayi Sallah da najasa a tufafi?
Fatawowin Rahama: KU KASANCE MASU GASKIA - Prof. Sani R/Lemo
2026/10/01
Fatawoyin Rahma
Ranar Asabar 15/4/1446-26/9/2026
Shimfida: _Ko Kusance Masu Gaskiya Tare Da Masu Gaskiya_
Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON
Tambayoyi da Amsoshi :
1. Menene hukuncin shimfiɗa darduma ta hanya mai dauke da hoton Ka’aba ko wata alama da take nuna alqiba?
2. Meye sa mutane suke rubata Abdulrahma da “L” maimakon Abdurrahman!
3. Hukuncin ‘yan Kasuwa ma su sa kaya a hanya da wurin amfanin mutane gaba ɗaya!
4. Za a iya yiwa gawa wanka a banɗaki!
5. Mutum zai iya koyan Al-qur’ani ta hanyar sauraro a cassette?
6. Hukuncin masu amfani da takardun wasu domin samun aiki?
7. Ya hallata mutum ya karanta Al-ƙur’ani ba tare da riga ba!
8. Ya hallacin albashin kwanaki da mutum ya yi ƙarya ya ɗauke su da uzurin ƙarya!
9. Mutumin da ya rabu da matarsa, zai iya karbar wasu daga cikin kayan Lefen da ya bata!
10. Menene ma’anar karya mace a Hadith Annabi (ﷺ)
11. Hukuncin nannade kaya in mutum zai yi Sallah?
12. Menene hukuncin sana’ar da wasu mata ke yi, inda suke sanar da cewa gobe za a yi awara ko makamancinta, Ana biyansu kafin suyi
Fatawowin Rahama: Q&A 19-09-2026 - Prof. Sani R/Lemo
2026/10/01
Fatawoyin Rahma
Ranar Asabar - 8/4/1448 - 19/9/2026
Tambayoyi da Amsoshi tare da _Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON_
Menene bambancin tsakanin Sallar Shuruq da Sallar Walaha!
Idan mamu ya samu raka’a uku tare da na gefe da shi, in ya tashi cikawa, na gefensa zai iya bin shi su cika tare?
Shin matar da take al’ada za ta shiga massallaci? In ta shiga za ta iya taba mushafi?
Hukuncin addu’a buƙata bayan Tahiyar ƙarshe!
Ya hallata iyaye su hana ‘ya’yansu aure ba wani dalili?
A daidai ina Ladan zai ce mutane su yi Sallah a gida in ana tsaka da ruwan sama?
Bambancin yanke Sallah da Sallamar fita daga Sallah!
Shin addinine ko al’ada - amare ba za su fita daga gidan aurensu ba har sai wani lokaci?
Matar da mijinta ya saketa saki biyu-kafin ta gama iddarta sai ya rasu- za ta yi masa takaba?
Hukuncin Sallah da Singeleti!
Za a iya bawa wanda ya mallaki nisanin Zakka, Zakka?
Mutumin da yake da lokacin da yake fitar da zakka, sa ya samu kyautar kuɗi a wani lokaci na daban , zai hada wannan kyautar a lissafin zakkarsa a lokacin da ya saba?
Hukuncin wanda yake cikin damuwa akan laifin da yayi duk da ya tuba!
Wanda yayi Umra sannan yake son ya sake yiwa wani, A ina zai ɗauko harama?
Fatawowin Rahama: Q&A 13/08/2026 - Prof. Sani R/Lemo
2026/09/27
Fatawoyin Rahma
Ranar - Lahadi 2/4/1448 - 13/9/2026
Tambayoyi da Amsoshi tare da Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON
1. Sakin da ake kome da sakin da ba a kome
2. Dole mace ta sanya hijabi in za ta yi aikin gida a tsakar gidan da akwai makwabta da suke bene za su iya hangota ta tagarsu?
3. Menene hukuncin kwanciyar rub da ciki!
4. Soja da aka tura shi aikin tsaro tsakanin Nigeria da Chadi na tsawon shekara ɗaya zai iya ƙasaru Sallolinsa a iya tsawon zamansa?
5. Shin zihari ne mace ta kira mijinta ‘yaya’ ko shi ya kirata ‘ƙanwata’
6. Mutum da ya tuno ana binsa ba shi bayan mutuwar wadanda suke bin shi bashi?
7. Hukuncin mace da aka cire mata da a cikin mahaifa, za ta cigaba da ibada?
8. Mutumin da yake son yin ibada amma shaidan yake masa wasuwasi cewa ba don Allah yake yi ba!
9. Hukuncin kallon fuskar mace yayin cinikaya!
10. Hukuncin fitsarin mace a tsaye!
11. Hukuncin wanda yayi Atishawa Liman ya na huɗuba!
12. Ana rama nafilar rawatib ta bayan Magriba in ya kubce ma mutum!
13. Idan aka hada Sallar Magriba da Isha, za a yi ratibin Sallar Magriba?
14. Ya hallata wanda suke Sallah a wajen sana’arsu, su hada Sallah sannan su cigaba da sana’oinsu?
15. Menene madogarar masu kiran Sallah kafin lokaci!
16. Da mutum yayi bara da ya nemi rancen kudi da ruwa, wanne ya fi laifi?
17. Yaya mutum zai yi mu’amala da mahaifiyarsa mai mu’amala da bokaye!
18. Yaya mace za ta yi da mijinta mai yawan “chatting” da mata?
19. Ya hallata mutum ya nemi a siya masa mota saboda ya inganta sanarsa; ya burge mutane da yake harka da su!
20. Yin sallah a hotel da ke kusa da Harami daidai yake da sallah a massallacin Harami?
Fatawowin Rahama: NASIHA GAME DA ZAƁE - Prof. Sani R/Lemo
2026/09/22
Fatawoyin Rahma
Asabar 1 /4/1448 - 12/9/2026
Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON
Shimfida : Nasiha ga Al’uma game da Zaɓe da Waɗanda za a Zaɓa!
Tambayoyi da Amsoshi:
1. In mutum ya ta shi daga bacci da Asuba, dole sai yayi wanka kafin yayi Sallah?
2. hukuncin walimar haihuwa!
3. Direba ya na tuƙa mota sai wani ya buge shi, sanadiyar hatsari ya rasu ( wanda ya dake mai motar)!
4. Hukuncin ma’akacin da in an aike shi sayo kaya, sai yake ƙara kuɗin akan yadda ya sayi kaya!
5. Matafiyi zai iya haɗa Sallallin da ake haɗasu yayi su a ƙasaru; sannan in ya je massallacin ya bi liman, ya cika Sallah?
6. Matafiyi zai iya yin Rawatib!
7. Mutum da ya yiwa Mace ciki sannan ya aureta daga baya, ɗan da aka samu zai ci gado?
8. Yaya iddar matar da tayi ɓari bayan kwana biyar da rasuwar mijinta
9. Wanene maraya a Musulunci
10. Yaya matsayin wanda bai yi nafila bayan Ɗawafi saboda ba a Sallar nafila bayan La’asar.
11. Wace irin cuta ce take zama annobar da take ɗaukar hukuncin annoba a sharia!
Youth and Challenges of Modern Era - Prof. Bashir Aliyu Umar
2026/09/17
Public Lecture Topic: Youth And The Challanges Of Modern Era
Tare da
*Prof. Bashir Aliyu Umar OON*
Daga Mahmud Tukur New Theatre, Bayaro University, Kano.
01-4-1448 13-09-2026
Fatawowin Rahama: ADDININ MUSULUNCI BAYA KARƁAR BIDI’A - Prof. Sani R/Lemo
2026/09/15
Fatawoyin Rahma
Ranar Asabar - 23/3/1448H – 5/9/2026
Tara da Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON
Shimfiɗa: Addinin Musulunci Ba Ya Karɓar Bidi’a
Tambayoyi da Amsoshi:
1. Wanda ya yi Istikhara, amma ya kasa cire son yarinyar da ya yi Istikharar a kanta daga zuciyarsa; menene hukuncin Istikhrarsa?
2. Hukuncin amfani da fasahar AI wajen ƙirƙirar bidiyo daga hotunan mutane domin sarrafa su.
3. Hukuncin yawan mafarkin mutuwa ga mace mai juna biyu.
4. Shin ya halatta mutum ya bawa Makocinsa Kirista aron abin hawa domin zuwa coci?
5. Mene ne hukuncin bashin da Gwamnatin Najeriya take bin ɗalibi har ya mutu bai samu aiki ba?
6. Shin ya kamata a yi jam’i na biyu a masallacin da yake da limami Ratibi?
7. Hukuncin matan da suke cire mayafi a wuraren bukukuwa a gan DJs!
8. Hukuncin wanda yake fama da lalura, ta yadda duk lokacin da ya yi tsarki sai wani abu ya fito daga gabansa.
9. Mene ne hukuncin taimaka wa ɗalibai wajen satar amsa don kar su faɗi Jarrabawa?
Fatawowin Rahama: Q&A 30-08-2026 - Prof. Sani R/Lemo
2026/09/10
Fatawowin Rahma
Ranar Lahadi
17/3/1448 - 30/8/2026
Tambayoyi tare da Amsoshi tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON*
1. Wacce hanya mutum zai bi ya zama ɗalibin ilimin hadisi!
2. Wanda ya samu raka’a ta ƙarshe a Sallar Magriba, yaya zai kammala Sallarsa?
3. Hukuncin wanda ya rikice ya kasa tuna raka’a nawa yayi?
4. Lamarin wadda in za ta yi Sallah sai ta ji kamar wani abu zai faɗo mata?
5. Hukuncin mutuwa a wurare masu falala?
6. Laifin wanda ya taimaka wajen zubar da ciki dai dai yake da wanda ya kashe wanda aka haifa?
7. Mutum zai iya yafewa wanda yake bi bashi da ya mutu ba sai ya fadawa iyalan mamacin ba?
8. Ya hallata mutum yayi sadaqa ga iyayensa da suka rasu!
9. Yaya mutum zai sa riba ga kayan da yake sayarwa!
10. Idan aka gina coci a Fili ba tare da izininsa mai filin ba, yaya magada za su yi?
11. Sallar ƙasaru ga matafiyi!
12. In mutum zai cutu a hanyar sa ta zuwa massallaci, zai iya Sallah a gida sannan kuma ya samu ladan wanda ya je massallaci?
13. Mamu zai iya ƙin bin liman da ya hada Sallah in mamun yana ganin sharuɗɗan haɗa sallolin ba su cika ba?
14. Yaya hukuncin Tela da yake aiki a shagon da wutar lantarki da aka janyo zuwa shagon ta sata ce?
15. Akwai addu’ar rufe gida ko daki?
16. Ana iya tofi da shafawa yaro yayin yi masa addu’a safe da yamma?
17. Mace za ita iya Sallah da zani da hijabi da ya rufe jikinta, ko da bata da riga?
18.kashin kaji najasa ne?
19. Hukuncin mutumin da aka bawa bashi da riba amma yake musun haka?
20. Hukuncin Wucewa gaban mamu ta kofar da aka bar ta a bude domin wucewar mutane!
21. Mace za ta iya Sujjadar Tilawa ba tare da hijabi ba?
22. Mutum zai iya azumin domin ya samu lada sannan ya rage kiba?
23. Mutumin da yayi alwala, yayi Azkar din bacci sannan ya sadu da iyalansa, sai ya sake Azkar?
24. Mutumin da yake Sallar dare, an ina ya kamata yayi addu’oinsa?
25. Yaya ya kamata musulmi ya gaishe da manya?
26. Akwai hadisin da ya ce za a fara sahu daga tsakiyar sahu?
Fatawowin Rahama: BACIN AQIDAR ‘HUMANITY’ - Prof. Sani R/Lemo
2026/09/08
FATAWOYIN RAHMA
Ranar Asabar
16/3/1448H – 29/8/2026
_Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON_
Shimfiɗa – ```Bacin Aqidar “Humanity”``
Tambayoyi da Amsoshi -
1. Menene hukuncin neman ruwa daga wurin wanda ba Musulmi ba domin yin alwala.
2. Shin mutum zai iya yin addu’a a Tahiya ta farko?
3. Menene matsayin addu’ar da ake yi bayan Tahiya?
4. Menene hukuncin fitar maziyyi ga mai azumi?
5. Mutumin da ya samu sallar jana’iza bayan an riga an yi kabbara ta farko ko ta biyu, daga wace kabbara zai shiga cikin sallar?
6. Menene hukuncin matafiyin da ya haɗa Sallar Azahar da La’asar a lokacin Sallar Azahar?
7. Menene hukuncin matafiyin da bai yi Sallar Azahar a ƙasaru ba har sai da ya dawo gida a lokacin Sallar La’asar? Shin zai yi Sallar Azahar a ƙasaru ne ko cikawa zai yi?
8. Mutumin da ya karɓi kuɗin ɗan’uwansa, bayan rasuwarsa, shin zai iya amfani da waɗannan kuɗaɗen wajen hidima ga iyalinsa, bisa hujjar cewa yana mayar da haƙƙin mamaci!
9. Menene hukuncin mutumin da yake karɓar albasa daga wanda suke zama tare, wani lokaci ya mayar, wani lokaci kuma ba ya mayarwa?
10. Menene hukuncin mutumin da yake yin Sallah a cikin shagonsa, kuma ba ya zuwa Sallar Jam’i?
Fatawowin Rahama: Q&A 9-8-2026 - Prof. Sani R/Lemo
2026/08/19
*Fatawoyin Rahma*
Ranar Lahadi
25/2/1448 - 9/8/2026
Tambayoyi da Amsoshi tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON*
1. Hukuncin Dillanci!
2. Mutumin da yake so wata, ita ma take sonsa, amma iyayensa ba sa son su tare; yaya zai yi?
3. Hukuncin wanda ya ci abinci yana azumi da mantuwa!
4. Hukuncin yin kyauta ga ma’akacin Immigration da yayi aikin yin passport ga mutumin da ya masa kyauta!
5. Hukuncin rage shekaru don a daɗe a na aiki?
6. Hukuncin kiwon dabbobi domin siyarwa Kiristoci lokacin bukkunansu!
7. Ya hallata mutum ya bibiyi ma’aikatu domin bankaɗo cin hancin da rashawa?
8. Hukuncin ta da iƙama bayan Kiran sallah-ba tare da tazara ba.
9. Yaya hukuncin tube mace tumbur a mata tiyata!
10. Hukuncin yara da ba sa turawa mahaifinsu kuɗi saboda ya na da kuɗi kuma mahaifiyar su ta umurce su da ka da su ta ra masa!
11. Ta yaya mutum zai bambance jarabawar da Allah ya masa saboda laifinsa da kuma jarabawar da Allah ya yi masa domin daukakar darajarsa!
12. Dole ne mutum ya san ma’anar adduar da ya ke yi?
13. Yaya ake yin Istikhara?
14. Za a yi salatin Annabi ﷺ a sallar nafila?
15. Wanda ya mutu ta hanyar nitsewa a ruwa ko gobara, za a masa wanka?
16. Shawara ga mai fama da matsanancin wasuwasi?
17. Hukuncin wanda yayi ƙarya akan halayyar wani mutum!
18. Yaushe ake “ as-sallatu khairul minannaum”?
19. Falalar Limanci?
20. Ana yin azumin kaffara ga wanda ba musulmi ba?
21. Hukuncin Jami’an tsaron da suke hana wanda aka tsare yin sallah!
Fatawowin Rahama: MUMINI BAZAI YI ZINA ALHALIN YANA MUMINI BA - Prof. Sani R/Lemo
2026/08/12
Fatawowin Rahma
Ranar Asabar
24/2/1448 – 8/8/2026
Tare da _Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON_
Shimfida: *Mumini ba zai yi zina alhali yana mumini ba…*
Tambayoyi da Amsoshi:
1. Sallar Ƙasaru ga mai aiki a wani ƙauye.
2. Lokacin Sallar Shurūƙ.
3. Shin wankan Idi ba ya wadatar da alwala?
4. Yaya wanda ya ci haramun a lokacin da yake aiki zai tuba?
5. Yaya ya kamata a raba littattafan addini da mahaifi ya barwa magadansa?
6. Ya halatta mutum ya roƙi Allah Ya so shi fiye da wani?
7. Mutumin da idan ya karɓi albashi, ya bawa mahaifiyarsa wani abu, sannan ya bawa matarsa sauran; amma matar ba ta gode masa. Wace nasiha za a yiwa wannan matar?
8. Su waye ɗaliban malami? Kuma waɗanda suke sauraron malami ta kafafen sada zumunta, za a iya kiran su ɗaliban malamin saboda suna sauraron karatunsa?
9. Idan mutum ya yi sallah a masallacin da ba a haɗa salloli a cikinsa, zai iya zuwa wani masallacin da ake haɗa salloli ya bi su?
10. A rayuwar aure, namiji ne kawai yake da haƙƙin neman kusantar matarsa, ko ita ma tana da wannan haƙƙin?
11. Mutum zai iya siyar da abin da baya hannunsa?
Fatawowin Rahama: Q&A 5-07-2026 - Prof. Sani R/lemo
2026/07/21
Fatawoyin Rahma
Ranar Lahadi 20 /1/1448 - 5/7/2026
Tambayoyi da Amsoshi tare da _Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON_
Mutumin da aka ɗauke shi aiki da sharaɗin zai zo tun ƙarfe takwas na safe zuwa ƙarfe biyar na yamma; zai iya tashi kafin ƙarfe biyar in ya gama aiki da aka sa shi?
Shin wanda ya je wajen boka ba da sanin boka bane, hukuncin ko yayi sallah na kwana 40 ba za a karba ba zai hau kanshi?
Wanda yayi Sallar Asuba a masallaci sai ya koma gida yayi zikiri har rana ta fito sannan yayi sallah raka’a biyu; zai samu ladan wanda yayi Hajji da Umra?
Mutum zai iya karbar Kwangilar aikin coci?
Mutumin da yayi zina ya tuba, Allah zai karbi tubansa ko da ba a masa haddi ba?
Hukuncin wanda ya ba da shaidar karatunsa ga wani ya yi amfani da takardun domin ya samu aiki da takardun!
Ya hallata mutum yayi addu’a da ayar Al-Kur’ani a cikin Sujjada?
Hukuncin sauraron waƙa!
Wanda suka sha ruwa saboda ladan ya kira Sallah kafin lokaci da kuskure; shin za su rama azumin?
Hukuncin mai gıda, mawadaci da ya dauki yaro aiki amma ba ya biyansa yadda ya dace!
Mutumin da yake shugabantar ma’aikata, zai iya ba kansa kwangila?
Mutumin da aka yi yarjejeniya da shi ba zai yi wani aiki ba, alhali albashin da ake ba shi ba ya isan sa; zai iya karya wannan yarjejinar ya nemi wani aiki!
Yaya hukuncin albashin wanda ya canza shekarun haihuwarsa yayin daukarsa aiki?
Mutum zai iya ware lokaci yayi karatun Al-Kur’ani domin ladan ya je ga mahaifarsa?
In mutum ya siffanta matarsa da wata dabba; hakan ma zihari ne?
Mutum zai iya amfanin da kudin ruwan Banki?
Yaya hallata mutum ya cigaba da zama da matarsa bayan ya kamata har sau uku tana tattaunawa da maza?
Ya hallata mutum ya bawa malaminsa Zakka?
Marar lafiya da ake bi azumi har na shekara uku, ya fara rama sai ciwon ya dawo, yaya zai yi?
Fatawowin Rahama: KISHIN ƘASA - Prof. Sani R/lemo
2026/07/12
*Fatawoyin Rahma*
Ranar Asabar 19/1/1448 - 4/7/2026
Tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON*
Shimfida : *Kishin Kasa!*
Tambayoyi da Amsoshi:
1. Mace za ta iya yin ɗawafi ko sa’ayi da niƙabi? Menene hukuncin kitso da yin lalle yayin Hajji ko Umra?
2. In mace ta yi allurar tsarin iyali sannan jini yana rikice mata; yaya za ta gudanar da sallarta?
3. Idan mai gyaran mota yana samun rangwame akan kuɗin abubuwan da za a gyra mota da ya karɓa daga wajen waɗanda suka kawo masa aikin gyran mota; ya hallata yayi amfani da rangwame da ya samu?
4. Hukuncin kuɗin ruwa da Bankuna suke bayarwa? Mutum zai iya aikin alhairi da kuɗin ruwa?
5. Yaya wanda yake da kaddarori daban daban zai fitar da Zakka?
6. Shin bandaki a ɗaki yana jawo aljanu?
7. Ya hallata mutum yayi mummunar addu’a ga azzalumin shugaba?
8. Yaya hukuncin fara alwala da Bismillah!
9. Hukuncin wanda ya karanta Fatiha a Sallah ba tare da Bismillah!
10. Menene hukuncin mace da ta gama jinin al’ada ta yi wanka, sai daga baya jini ya dawo, yaya za ta yi?
11. Wace addu’a ake yiwa yara Safiya da Maraice don neman kariya?
12. Hukuncin amfani da sunan Mahaifin da ba naka ba
*Domin Samun karatukan Malam ku bibiyi wannan shafuka:*
Facebook: https://www.facebook.com/Drmuhdsaniumarmusa/
Twitter: https://twitter.com/DrMSaniR_Lemo
Instagram: https://www.instagram.com/drmsanirijiyarlemo
Telegram:https://t.me/drmsaniumar
YouTube: https://youtube.com/channel/UCa9nK0j55mr9PPhv4k3Wmbw
Website:http://www.drmsanirijiyarlemo.net
*Domin Sauke Manhajar Tafsirin Alƙur'ani :*
Android: https://play.google.com/store/apps/details?id=online.smartech.basayir.hausa
Apple : https://apps.apple.com/us/app/maanoni-da-shiriyar-alqurani/id6480479512
https://sanachannelstv.wuiltweb.com/
*Domin Tallafa wa Asusun Sautul Haq:*
Account Number: 0010885007
Taj Bank
Account Name: AL - IMAMUL BUKHARI CENTER FOR RESEARCH AND TRAN
Fatawowin Rahama: JUYAWAR ZAMANI - Prof. Sani R/Lemo
2026/06/27
*Fatawoyin Rahma*
Asabar 5 Al-Muharam 1448 - 20 June 2026
Tare da Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON
Shimfida: *Juyawan Zamani*
Tambayoyi & Amsoshi
1. Hukuncin shiga maqabarta da Takalmi!
2. Hukuncin shiga massallaci ga mai warin ciwo!
3. Wadda ta yi rashin lafiya a Ramadhan, sannan bayan ta warke kafin ta rama sai ta rasu, ‘ya’yanta za su rama mata?
4. Akwai zikiri da mutum zai karanta in zai hau ko sauka daga bene?
5. Ina hukuncin wanda zai yi wasu sunnonin Rawatib, ya bar wasu?
6. Menene hukuncin wannna addua’ar ga mamaci “Allah ya jaddada masa rahma”?
7. Mutum zai iya yiwa mahaifinsa da ya rasu Umra?
8. Matsayin mijin da yake zaune da matarsa a in da yake aiki, sannan sai bayan lokaci mai tsawo yake zuwa wajen ɗaya matarsa da take wani gari?
9. Hukuncin wanda ya manta yana azumi ya sha ruwa sau biyu ko sau uku?
10. Idan mutum ya riski Sallah da liman da yayi sahwu, ko da bai riski lokacin da yayi sahwun ba, zai bi liman yayi sujjadar sahwu?
11. Menene ma’anar maganar da ake cewa in an yi mutuwa “Allah ya sa Annabi ya san da zuwansa”
**Domin Samun karatukan Malam ku bibiyi wannan shafuka:*
Facebook: https://www.facebook.com/Drmuhdsaniumarmusa/
Twitter: https://twitter.com/DrMSaniR_Lemo
Instagram: https://www.instagram.com/drmsanirijiyarlemo
Telegram:https://t.me/drmsaniumar
YouTube: https://youtube.com/channel/UCa9nK0j55mr9PPhv4k3Wmbw
Website:http://www.drmsanirijiyarlemo.net
https://sanachannelstv.wuiltweb.com/
*Domin Sauke Manhajar Tafsirin Alƙur'ani na Fayyataccen Bayani :*
Android: https://play.google.com/store/apps/details?id=online.smartech.basayir.hausa
Apple : https://apps.apple.com/us/app/maanoni-da-shiriyar-alqurani/id6480479512
Website:
https://hausaquran.net/app/sura/1
*Domin Tallafa wa Asusun Sautul Haq:*
Account Number: 0010885007
Taj Bank
Account Name: AL - IMAMUL BUKHARI CENTER FOR RESEARCH AND TRAN
Fatawowin Rahama - Q&A 14-6-2026 - Prof. Sani R/lemo
2026/06/20
Fatawowin Rahma
Lahadi 28/12/1447 - 14/6/2026
Tambayoyi da Amsoshi tare da *Prof. Muhammad Sani Umar R/Lemo, OON*
Yaya hukuncin auren film!Mutumin da yake bin bashi zai iya sayar da kayan wanda yake bi bashi domin ya karɓi haƙƙinsa?Mutum zai iya karanta Al-ƙur’ani domin ladan ya kai ma mahaifansa?Yaya hukuncin yin Sallah a zaune?Mutimin da yayi wasa da Sallah da Azumi amma daga baya ya tuba, yaya zai yi? Sannan yaya zai yi da haƙƙin mutane da ya ci a baya?In wani zai yanka wa mutum dabbar layya, sai ya ambaci sunansa? Wanda yake fama da lalurar ‘spinal cord injury’ hannuwansa ne kadai ke yin motsi, zai iya yin taimama?In mutum yayi wa Iyayensa layya , shi ma zai samu laddan yin layyar?Kyautar da ake bawa iyalan mamaci zata shiga gado?Yaron shago zai iya sayan POS da kudinsa ya sa a jarin sana’ar sa?Hukuncin ilimin taurari!Mahaifiya za ta iya hana ɗanta sada zumunci?Mutum zai iya sanya Bluetooth yana sauraron Al-kur’ani har yayi bacci?Za a iya karbar tallafi a wajen mutumin da yake ba da tallafi ga ƙungiyoyi masu gudanar da ayyukan Asibiti, ko da babu asibitin amma an haɗa baki da wani mai Asibiti za a yi amfani da Asibitin sa domin samun tallafin?Matafiyi da ya bi mazauna gida Sallar Azahar zai iya tashi yayi sallar La’asar Ƙasaru?Ana iya ramawa mamaci Salloli da Azumi!Yaya za a samar da adalci a mu’amalar kasuwanci!Yaya hukuncin karanta littafin fassara mafarki na Ibn Sirin!Hukuncin aske gemu!Za a iya bin masbuqi Sallah?