
Advertise on podcast: Ilimi Hasken Rayuwa
This podcast has
28 episodes
Language
EnglishPublisher
RFI HausaExplicit
No
Date created
2015/07/07
Latest episode
2026/04/22
Average duration
10 min.
Release period
9 days
Description
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’Adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
Unlock Ilimi Hasken Rayuwa podcast Email contact info,
Listeners & Audience details
Email contact information
Direct podcast contact details

Listeners
Audience numbers & engagement insights

Audience details
Podcast Insights

Social media
Check Ilimi Hasken Rayuwa social media presence
Podcast episodes
Check latest episodes from Ilimi Hasken Rayuwa podcast
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2
2026/04/22
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tambayar.
Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..............
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2
2026/04/21
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tambayar.
Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna..............
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu
2026/04/14
A arewacin Najeriya, shigar mata makarantun yaki da jahilci ya fara ne a matsayin wani yunkuri na inganta rayuwar iyali da kuma tarbiyyar yara, inda mata da dama sun fahimci cewa rashin ilimi na hana su taimaka wa yaransu wajen karatunsu na zamani da kuma kulawa da lafiyarsu.
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Wani matashi ya yi nasarar ƙera jirgi marar matuƙi a jihar Kano
2026/04/07
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon, ya yi dubi ne kan yadda wani matashi a jihar Kanon Najeriya ya ja hankalin jama’a, bayan ƙirƙirar jirgi maras matuƙi, daidai lokacin da matasan wannan ƙasa ke faɗi tashin yadda za su samo masu ɗaukar nauyin ayyukan fasahar da suke son cimmawa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruwa...........
Yadda wasannin na'ura kwamfita ke samun karɓuwa a tsakanin matasa
2026/03/31
Shirimmu na ilimi hasken rayuwa na wannan mako yayi karin bayani akan wasannin na’ura kwamfuta masu kama da gaske da aka fi sani da virtual reality a turance.
Danna alamar sauti domin sauraron karin bayani........
Tasirin faɗowar wasu sinadarai daga sama a fagen kimiyya da fasaha
2026/03/03
Shirin "Ilimi Hasken Rayuwa" na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya yada zango ne a Jamhuriyar Nijar inda abaya-bayan nan aka rika samun fadowar wasu abubuwa daga sararin samaniya, lamarin da ke ci gaba da faruwa a sassan a kasar.
A baya bayan ne dai wasu abubuwa suka fado daga sararin samaniya a kauyuka 5 daban daban a yankin Kornaka, da Dakwaro da suka hada da Dan Madi, Baushi, da sauransu, haka abin ya taba kasancewa a 2021 inda aka samu wani babban dutse da ya fado daga sama a garin Aikawa na yankin Gazawa sannan, an samu wasu duwatsun a yankin Tanut, Agades da sauran yankunan Nijar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
Ra'ayoyi sun banbanta kan amfani da fasahar AI wajen yin tiyata
2026/02/24
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako a wannan makon, ya mayar da hankali kan binciken da ya gano cewa shigar fasahar AI cikin fannin tiyata na haifar da wasu matsaloli masu kama da barazana ga rayuwar ɗan adam, kan haka ne ma muka zanta da masana a fannin kimiyya da kuma ɓangaren lafiya, inda muka jiyo ra’ayoyin mutane game da yadda wasu ke yarda AI ya duba lafiyarsu har ta kai ga tiyata a wasu lokutan.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Yadda satar jarabawa ke taka rawa wajen kassara ingancin ilimi a Najeriya
2026/02/17
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda satar jarabawa ke ƙoƙarin zama ruwan dare a makarantun sassan Najeriya, matsalar da ke ci gaba da illa ga ingancin ilimi a dukkan makarantu na ƙasar.
Akwai zarge-zargen da ke nuna cewa wasu daga cikin jami'an hukumomin da ke kula da shirya jarabawa a matakai daban-daban na taimakawa wannan mummunar ɗabi'a ta satar jarabawa ta hanyar fallasa amsoshin tambayoyin da ake shirin fitarwa ga ɗalibai.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Yadda masu larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a Najeriya
2026/02/10
Shirin na wannan mako ya ba da hankali ne akan yadda masu fama da larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a wasu sassan Najeriya.
Ana fuskantar koma bayan koyan harshen larabci a arewacin Najeriya
2026/02/03
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali ne kan dalilan da suka haddasa rashin koyon ingantaccen larabci tsakanin daliban sakandare a arewacin Najeriya, sabanin lokutan baya.
A shekarun baya, alkaluma sun nuna cewa kusan kaso hamsin na larabcin da Dalibai ke koya suna samun sa ne a makarantun boko ba lallai sun sun halarci makarantun Arabiya, al’amarin dake neman zama tarihi a wannan zamani.
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
Yadda satar jarabawa da cin hanci da rashawa ke kassara ɓangaren Ilimi a Kamaru
2026/01/27
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani bincike can a Jamhuriyyar Kamaru ya gano yadda satar Jarabawa da cin hanci da rashawa ke mummunan tasiri a ɓangare ilimin ƙasar.
Matsalar ta cin hanci da rashawa kai tsaye ta yi mummunar illa ga yanayin ɗaukar malamai aiki da gina makarantu ko kuma samar da ci gaba a ɓangaren na Ilimi, yayinda a gefe guda satar jarabawar da ɗalibai ke yi ke zagon ƙasa ga makomar ilimi a ƙasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Makomar karatu a yankin arewacin Najeriya cike da barazanar ƴanbindiga
2026/01/20
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan makomar karatun ɗalibai a makarantun Najeriya musamman yankin arewaci mai fama da matsalolin tsaro, dai dai lokacin da aka koma sabon zangon karatu Iyaye na cike da fargaba kan tsaro a makarantu.
Makwanni gabanin tafiya hutun zangon da ya gabata cikin watan Nuwamban bara ne, hare-haren ƴan bindiga suka tilasta kulle makarantu a sassan arewacin Najeriyar ciki har da makarantun Unity da ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin Tarayya.
Wasu na da ra'ayin cewa sai an haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin dukkanin ɓangarori ne, ɗalibai za su samu cikakken tsaro a makarantu tare da samun ɗorewar Ilimi a yankin.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Kashi na biyu kan yadda sabuwar manhajar fassarawa da lissafa haraji ke amfani a Najeriya
2026/01/06
A kashi biyu na shirin ilimi hasken rayuwa, mun ɗora kan sabuwar manhajar fassarawa da da sauƙaƙa lissafin karɓar haraji.
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Faruk Yabo.
Farfesa Aminu Bello ya samar da manhaja mai sauƙaƙa lissafin haraji a Najeriya
2025/12/30
Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna da Farfesa Aminu Bello Usman daga Birtaniya, ɗan jihar Kano da ke tarayyar Najeriya, wanda ya ƙirƙiri wata Manhaja da za ta taimaka wa mutane wajen sauƙaƙa musu lisaffin hada-hadar kuɗaɗe musamman ma na haraji.
Wani abin ban sha’awa dangane da Manhajar da aka fi sani da Software a Turance, shi ne yadda wannan manhajar ta ƙunshi harsuna biyar.
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Nasir Sani.
Akwai bukatar samarwa masu buƙata ta musamman ayyukan yi domin dogaro da kai
2025/12/23
Mutane da suka tsinci kansu a cikin masu buƙata ta musamman sakamakon nau’ikan nakasar da suka fama da ita sun share shekaru suna fuskantar giɓi babba a muhimman fannonin rayuwa daban daban, ciki kuwa har da samun guraben ayyukan yi ko da kuwa a ce sun yi katarin tsallake shingen samun ilimi, matsalar da ta fi ƙamari a ƙasashe masu tasowa ciki har da na Nahiyar Afrika.
Mutane da suka tsinci kansu a cikin masu buƙata ta musamman sakamakon nau’ikan nakasar da suka fama da ita sun share shekaru suna fuskantar giɓi babba a muhimman fannonin rayuwa daban daban, ciki kuwa har da samun guraben ayyukan yi ko da kuwa a ce sun yi katarin tsallake shingen samun ilimi, matsalar da ta fi ƙamari a ƙasashe masu tasowa ciki har da na Nahiyar Afrika.
Kan wannan batu shirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan lokaci zai tattauna, bayan da ya yi tattaki zuwa Jihar Jigawa da ke tarayyar Najeriya, akan ƙorafin da wasu fama da nakasar suka yi a bisa ganin cewar suna neman rasa damar samun guraben ayyukan yi da suka cancanci dafewa.
A latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
Podcast reviews
Read Ilimi Hasken Rayuwa podcast reviews
Podcast sponsorship advertising
Start advertising on Ilimi Hasken Rayuwa relevant audience podcasts
You may also like to advertise on these Podcasts

5435
Yarn | A Story Podcast
John Roche

00181
Produced By
Tomas Loucky

00339
this is property
John Pidgeon & Rachelle Kroon

0064
LÄNGER GUT LEBEN - mit Diane Hielscher
Diane Hielscher & BosePark

00105
The World’s Team
The World’s Team

00235
CEO's You Should Know - Pittsburgh
iHeartRadio Pittsburgh

00775
Omelie : live ogni domenica
BG live

00339
Julia Tulipans' Evolution Radio Show
Julia Tulipan, Mag. Julia Tulipan

11251
Levels with Willie Mason & Justin Horo
Levels Network

5396
1080 KRLD In-Depth
Audacy


