1016968670
Lafiya Jari ce

Advertise on podcast: Lafiya Jari ce

Categories
Country
United States
This podcast has
25 episodes
Language
English
Publisher
RFI Hausa
Explicit
No
Date created
2015/07/07
Latest episode
2026/10/12
Average duration
11 min.
Release period
8 days

Description

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.

Unlock Lafiya Jari ce podcast Email contact info,
Listeners & Audience details

Email contact information

Direct podcast contact details

Listeners

Audience numbers & engagement insights

Audience details

Podcast Insights

Social media

Check Lafiya Jari ce social media presence


Podcast episodes

Check latest episodes from Lafiya Jari ce podcast


Ƙalubalen lafiyar da matsalar birkicewar al'ada ke haifarwa ga mata
2026/10/12
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi nazari kan matsalar birkicewar al’ada a tsakanin mata, matsala ce da ke matsayin ruwan dare a wannan zamani lura da cewa kusan dukkanin 1 cikin mata 3 akan iya samunta da wannan matsala wadda kuma ba safai aka fiya mayar da hankali akanta ba, duk kuwa da ƙalubalen hakan ga lafiyar mata. Mata da dama ne dai suka shafe shekaru suna fama da matsalolin da suka shafi al’ada amma ba tare da samun waraka ba, hakan ya sanya yawaitar ƙorafe-ƙorafe nan da can. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Yawaitar ɓarkewar cutar Diptheria a sassan jihohin Najeriya
2026/10/05
A wannan makon shirin ya yi duba kan cutar Diptheria, ko kuma mashaƙo, cutar da a baya-bayan nan ake yawan ganin ɓarkewar annobarta a wasu sassa na jihohin Najeriya wadda kuma ke kisan ɗimbin mutane baya ga kwantar da dama a asibitoci, inda wasu alƙaluma ke cewa daga watan Janairu zuwa Agustan shekarar nan mutane dubu 16 da 997 suka kamu da cutar a sassan Najeriya. Masana sun yi ittifaƙin cewar mashaƙo ko kuma Deptheria tafi shafar yaran da ba a yiwa rigakafin cutuka ba ƴan shekara 1 zuwa 14 kodayake a wasu lokutan akan samu hatta waɗanda aka yiwa rigakafin sun kamu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Rawar da Ungozomar gargajiya ke takawa wajen ceton rai a yankunan karkara
2026/09/28
Goyon ciki da haihuwa na cikin mayan ƙalubalen Lafiyar da suka addabi ƙasashe masu tasowa irin Najeriya, ta yadda a kowacce rana ake ganin mutuwar ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko kuma renon ciki, baya ga tarin jarirai da ke rasa ransu. A irin wannan yanayi galibi Ungozomar gargajiya ke matsayin masu ceto a irin wannan yanayi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.............
Lafiya Jarice: Muhimmancin tazarar haihuwa ga lafiyar uwa da jaririnta
2026/09/21
Bisa ga zubin halittar ɗan adam kowacce mace kan iya haihuwa aƙalla sau 15 zuwa 30 a tsawon rayuwarta, a wani yanayi da ƙasashen Afrika ke sahun gaba wajen yawan haihuwar, kodayake liktoci na jan hankali game da muhimmancin bayar da tazara ko kuma hutu koma taƙaita haihuwar baki ɗaya saboda dalilai na lafiya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Mata dubu 14 ke kamuwa da cutar kansar mahaifa a Najeriya duk shekara-Rahoto
2026/09/14
Shirin Lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan cutar dajin mahaifa da ke addabar mata musamman a Nahiyar Afrika. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashi Aminu.
Illar da ke tattare da shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba
2026/09/07
Shirin lafiya jari ce a wannan karon ya mayar da hankali kan ɗabi'ar shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba, wanda a turance ake kira Self-medication da kuma illar hakan ga lafiyar jama’a. Wasu alƙaluma sun nuna cewa fiye da kashi 70 cikin ɗari na ƴan Najeriya ne yanzu haka sun bijirewa ziyartar asibitoci ta yadda suke shan magungunan tarin cutuka ba tare da umarnin ƙwararru ba, musamman a ɓangaren cutukan da suka shafi zazzabin cizon sauro da ciwon kai da kuma tari baya ga ciwon gaɓoɓi ko ma ciwon ciki dama ciwon kunne ko ciwon haƙori da sauransu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.............
Yadda cutar damuwa ke zama ruwan dare a tsakanin al'umma
2026/08/24
A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce zai yi duba ne kan lalurar Depression ko kuma damuwa mai tsanani a harshen hausa, cutar da ke ƙoƙarin zama ruwan dare tsakanin al’umma a baya-bayan nan, wataƙila ko saboda yanayi da matsin rayuwa. Ku danna almar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Yadda wuraren saida magunguna ke samun karbuwa a jamhuriyar Nijar lokacin damuna
2026/08/17
Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya leƙa jamhuriyyar Nijar inda ya yi dubi kan yadda ake samun kafuwar wuraren saida magunguna birjik musamman a lokaci irin na damuna, wato dai lokacin da ake ganin yawaitar cutuka irin zazzaɓin cizon sabro. Danna alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
Yadda cutar kwalara ta jefa ɗumbin mutane cikin firgici a jihar Bornon Najeriya
2026/08/10
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sake ɓarkewar cutar kwalara ko kuma amai da gudawa a jihar Borno, lamarin da ya jefa ɗimbin jama’a a yanayi na matuƙar damuwa damuwa musamman bayan da rahotanni ke cewa an samu yaɗuwar annobar cutar har a yankunan da ake ajje da ɗimbin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu.
Yadda cutar Bilharzia ko Tsagiya ke barazana ga rayuwar ɗimbin ƴan Afirka
2026/08/03
A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba duba kan cutar Schistosomiasis (shustosumayusus) ko Bilharzia koma Snail fever kamar yadda wasu ke kiranta, cutar nan dai da aka fi sani da tsagiya a hausance, cutar alƙaluma ke nuni da cewa kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da ita na a nahiyar Afrika. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......
Yadda farashin magunguna ke tashi a lokacin damuna da aka fi fama da cutuka
2026/07/27
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi dubi ne kan yawaitar cututtuka a irin wannan lokaci na damuna, daidai lokacin da bayanai ke nuni da cewa farashin magunguna ya yi tashin gauron zabbi. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...
Yadda gwamnatin Kano ta yi nasarar rage mace-macen mata a lokacin haihuwa
2026/07/20
Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu  ya mayar da hankali kan nasarar da jihar Kano ke iƙirarin samu bayan fitar wani rahoto da ke cewa an samu raguwar mace-macen mata a lokacin haihuwa a sassan jihar wadda a baya ke sahun gaba wajen asarar rayukan ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko goyon ciki Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin..........
Matsalar ƙarin mahaifa ko fibroids ga lafiyar mata
2026/07/13
Shirin Lafiya Jari Ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar ƙaba ko ƙarin mahaifi ko kuma fibroids da ke addabar tarin mata ta yadda da dama ke rayuwa da shi ba tare da sani ba, yayinda wanzuwarsa a mahaifa kan haddasa matsala ga yanayin haihuwa ga matan. Galibi mata a tsakanin shekaru 35 zuwa 37 ne suka fi kamuwa da wannan lalura ta Fibroids, a wani yanayi da ƙididdiga ke cewa kaso mai yawa na mata na fara gamuwa da ɓirɓishin lalurar ne tun daga lokacin da suka haura shekaru 20 a duniya. A baya-bayan nan ana yawan ganin matan da ke ƙorafi kan lalurar ta Fibroids ko kuma ƙarin mahaifa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Yadda cutar Typhiod ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Afirka da Asiya
2026/07/06
Shirin na Lafiya Jari ce zai  a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan zazzaɓin Typhoid, cuta mai haɗari wadda ƙwayar cutar Salmonella Typhi ke haddasawa, inda ta kan yaɗu ta hanyar abinci ko ruwan da ya gurɓata. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
Ƙaruwar masu fama da cutar sikila a Jamhuriyar Kamaru
2026/06/29
A wannan makon shirin ya yi duba ne kan ƙaruwar masu fama da cutar sikila a jamhuriyyar Kamaru bayan fitar wani rahoto da ke cewa cikin shekara 1 kaɗai an tattara alƙaluman sabbin mutum dubu 6 da aka gano suna ɗauke da cutar. Wannan cuta mai alaƙa da nau’in jini, na daga cikin matakan yaƙi da ita shi ne tabbatar da gwaje-gwajen jini tun kafin aure don kaucewa haifar yara masu ɗauke da ita, ganin cewa hanya ɗaya tal ta samun masu cutar shi ne ta hanyar gado wato daga iyaye.

Podcast reviews

Read Lafiya Jari ce podcast reviews


0 out of 5
0 reviews

Podcast sponsorship advertising

Start advertising on Lafiya Jari ce relevant audience podcasts


What do you want to promote?