Muhallinka Rayuwarka

Advertise on podcast: Muhallinka Rayuwarka

Categories
This podcast has
25 episodes
Language
Publisher
Explicit
No
Date created
2015/07/07
Latest episode
2026/04/19
Average duration
20 min.
Release period
15 days

Description

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

Unlock Muhallinka Rayuwarka podcast Email contact info,
Listeners & Audience details

Email contact information

Direct podcast contact details

Listeners

Audience numbers & engagement insights

Audience details

Podcast Insights

Social media

Check Muhallinka Rayuwarka social media presence


Podcast episodes

Check latest episodes from Muhallinka Rayuwarka podcast


Matasan kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada suka kai rangadi a Nijar
2026/04/19
A yau shirin zai leka jamhuriyar Nijar ne inda matasa daga kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada da zaizayewar kasa don mayar da yankin tsanwa suka kai rangadi a Nijar musaman a Jihohi 5 na kasar da suka hada da Tillaberi Niamey, Dosso, Maradi da Zinder don duba irin cigaban da Nijar ta samu a wannan fannin da nufin kwaikwayonsa don kaddamar da shi a kasashensu.
more
Dalilan da suka sanya Manoma Albasa a Nijar fuskantar ƙalubale a bana
2026/04/14
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon, ya yi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda aka fuskanci ƙalubale kan noman Albasa a shekarar bana. Bayanai daga ƙasar ta Nijar na cewa a halin da ake ciki, Manoma da dama sun shiga halin ƙaƙa-ni-kayi saboda rashin samun kuɗaɗen shiga, la'akari da irin rawar da noman na Albasa ke taka wa wajen sama musu abin kashewa.
more
Yadda sare itace a Nijar ke haifar da koma baya wajen samun amfanin gona
2026/04/04
Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ake samu canjin yanayi ta hanyar saran icen "Gawo" barkatai daga Makiyaya da su kansu Manoman, wanda ake ganin ke haifar da koma baya wajen samun yalawar abinci kamar, bakamar yadda aka saba ba a shekarun baya a cikin gonaki na Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..........
more
Hukumar NIMET ta yi hasashen samun saukar ruwa da wuri a daminar bana a Najeriya
2026/03/14
Shirin ‘Muhalinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya mayar da hankali kan hasashen ruwan sama da Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya NIMET ta yi, gabanin kamawar daminar bana, inda ta bayyana cewa damina za ta sauka da wuri a jihohi irin su Kano da Niger da Rivers da wasu jihohi 12 na ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..............
more
Yadda cutar tumatiri ta kasara manoma a wasu jihohin arewacin Najeriya
2026/01/31
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ tare da Michael Kuduson a wanan  mako ya yi duba kan  wata mummunar cutar tumatiri da ake kira Tuta Absoluta ko kuma cuta mai karya garkuwar tumatir. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
more
Dalilan da masana suka ce su ke ƙara bayyana sauyin yanayi
2026/01/11
Shirin muhallinka rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne  kan yadda sauyin yanayi ko dai na zafi ko na sanyi ko kuma damina ke bayyana ƙarara, musamman a yankin yammacin Afirka. Ga misali a Najeriya, ɗaya daga cikin sauye-sauyen yanayin da aka shaida shi ne rashin hunturu a shekarar  bana, musamman a Yankin arewacin ƙasar, inda aka saba ganin kankamar Yanayin na sanyin mai tsanani daga ƙarshen watan Nuwamba ko farkon Disamba zuwa ƙarshen watan Janairu ko farkon Fabarairu. Gabanin fuskantar wannan lamari dai hatta yanayin damina da lokacin zuwanta ya sauya daga abinda aka saba da shi, batun da hatta a wasu wuraren da ke yankin Kudu maso yammacin Najeriya ma an shaida hakan. Tuni dai wannan al’amari na sauyin lokutan yanayin zafi da damina ko kuma sanyi ya zama abin tattaunawa a tsakanin jama’a dangane da dalilan da suka janyo hakan, da dai wasu sauran tambayoyi da ake da ƙishirwar neman amsoshinsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Nura Ado Suleiman............
more
Noman rani na fuskanta barazana a Najeriya sabida tsadar kayan noma irinsu taki
2025/12/13
Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne Tarayyar Najeriya, inda ya duba irin barazanar da  noman rani ke fuskanta, musamman a wannan lokaci da farashin kayyakin gona suka faɗi warwas a yayin da farashin taki da sauran mahimman kayakin da ake amfaani da su wajen noman suke a can ƙololuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Michael Kuduson..........
more
Yadda manoman Jamhuriyar Nijar ke fama da ɓarnar makiyaya a ƙarshen damina
2025/11/29
Shirin muhallinka rayuwarka na wannan karon zai mayar da hankali ne kan irin fama da ake sha a karshen damina tsakanin manoman da suke tattarar Kayan gona da makiyayan dake dawowa daga kiwo zuwa wuraren da ake aikin noman a  wasu sasaan Jamhuriyar Nijar. A duk karshen damana makiyayan da suka tafi mashekari wurin kiwon dabbobinsu inda ke da isassar ciyawa nesa da gonaki na sabkowa wuraren da ake aikin noma don ganawa da jama'a, sannan da samun sauran tarikicen da manoman suka bari a gonakansu. Sai dai a irin lokacin na komawar makiyayan ana samun rikicin dake faruwa ' tsakaninsu da manoman da ba su ida tattare Kayan da suka noma ba, kuma da yanda wasu makiyayan ke saurin komowa a lokacin da manoman ke tsaka da aiki, duk da an tanadi dokar da ta tsaida komi a kasar ta Nijar.
more
Abubakar Ibrahim kan taron sauyin yanayi na COP30 da ke gudana a Brazil
2025/11/15
An buɗe taron Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi da ake kira COP 30 a Brazil inda masana muhalli da sauyin yanayi daga kasashen duniya za su mayar da hankali da kuma samar da dabaru kan sauyin yanayi. Za'a kwashe makwanni biyu ana gudanar da wannan taro wanda zai mayar da hankali a kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a kan wannan matsala.
more
Yadda wani ruwa da ke ɓulɓulowa ta ƙasa ke zubar da gidaje da kashe bishiyu a Nijar
2025/11/08
Shirin muhallinka rayuwarka na wannan yau zai maida hankalin ne kan wani ruwan dake bullowa daga kasa Wanda ya yi sanadiyar zubewar gidaje da kashe bishiyoyi da ga gurbata hanyoyi a unguwar Garin Malam ta Damagaram a Jamhuriyar Nijar. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.
more
Barazanar wutar daji da ke lakume gonakai a Jamhuriyar Nijar
2025/11/01
A cikin wannan shirin ,za mu leko Jamhuriyar Nijar inda a duk shekara ake fuskantar barazanar wutar daji da ke lakume gonakai da cimaka. Hukumomin Nijar sun dau matakai domin kawo karshen  wannan al'amari da manoma da kuma jama'a ke kuka  a kai.
more
Yadda manoma suka karkata akalar noman barkono bana a Najeriya
2025/10/25
Shirin wannan makon zai tare ne a jihar Kano dake Tarayyar Najeriya, inda aka samu manoma da dama a wasu yankuna da suka duƙufa wajen noman barkono a wannan shekarar. Ba shakka sun yi aiki tuƙuru, kuma haƙarsu ta cimma ruwa duba da ɗimbim barkono da suka girba. Wannan lamari dai ya tayar da hankalin waɗannan manoma, waɗanda sun sauya alƙibla ne saboda ganin yadda farashin amfanin gona dangin hatsi ya faɗi warwas a kasuwanni, kuma sun yi haka ne domin su more daga ribar da aka yi ta ci daga barkono, amma sai gashi lamarin ya yi musu ta leƙo ta koma. A kusan ilahirin kasuwannin kayan gwari, gani za ka yi ga barkono, wanda kafin yanzu yake tamkar gwal, sai ga shi yanzu masu saye su na mai tayin da suka ga dama. Masana sun yi ittifakin cewa, ba shakka rashin tsari da alƙibla wajen noma da kuma binciken halin da kasuwa  ke ciki sun taka rawa ainun a wcikin wannan matsala da aka samu. Sai dai kuma, matsaloli na yanayi ma sun taka irin nasu rawar, domin akwai matsin lamba daga yadda tsarin ruwan sama ya sauya, da sauraan matsaloli da suka addabi ƙasar noma. Matsalar yanayi da muhalli na mummunan tasiri akan ko wane irin nau’i na noma. shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin, tare da Michael Kuduson.
more
Masana game da fallen da ke bai wa ɗan Adam kariya daga sinadaran hasken rana
2025/10/19
A wannan makon, shirin zai mayar da hankali ne akan wani rahoton da masana suka fitar, wanda ke nuna cewa fallen nan ko shimfidar da ke bai wa ɗan Adam kariya daga wasu sinadaran hasken rana masu haɗari, da ake kira Ozone Layer, wanda kafin yanzu ake bayyana damuwa a game da lalacewar da ya fara yi, sakamakon ayyukan da ɗan Adam ke aiwatarwa ya fara gyaruwa. Sai ku biyo mu domin za mu tattaunawa da masana, shehunnan malamai akan wannan maudu’i. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin 'MUHALLINKA RAYUWARKA' tare da Michael Kuduson.......
more
Alfanun cibiyar bunƙasa noma a jihar Kano ga ci gaban samar da abinci a Najeriya
2025/10/11
Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Michael Kuduson a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda aka samar da wata katafariyar cibiyar bunƙasa harkokin noman Damuna dana Rani ga al'ummar jihar Kano wadda aka samar a garin Kadawa da ke ƙaramar hukuamr Garin Malam. bayanai sun ce wannan cibiyar bunƙasa noma na ƙunshe da tarin kayakin buƙata a lokacin noman walau na rani ko kuma na damuna duk dai a ƙoƙarin haɓaka harkar noma a jihar ta Arewa maso yammacin Najeriya. Bankin Musulunci da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kanon ne suka samar da wannan cibiya wadda ta laƙume biliyoyin dalolin Amurka ƙarƙashin shirin KSSB na haɓaka noma bisa kulawar SASAKAWA. Ku latsa alamar tsari don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.....
more
Yadda manoma a Jahuriyar Nijar suka koma noman Gyaɗa da Gujiya gadan-gadan
2025/09/27
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda manoma a Nijar suka koma noman Gyaɗa da riɗi gadan-gadan bayan sun yi watsi da shi tsawon shekaru, saboda matsaloli da noman ke fuskanta.Maraɗi ce kan gaba a noma Gyada ko Gujiya shekaru aru aru, sai Zinder da kuma Doso, waɗanda suka taimaka wajan hada-hadar kasuwancin Gyaɗa har a Kano inda ake tattara Dalar Gyadar.Yawan noman Gyadar ne ma ya sa turawan mulkin mallaka suka kafa masana’antar sarrafa man Gyada a 1943 a Maraɗi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson...........
more

Podcast reviews

Read Muhallinka Rayuwarka podcast reviews


0 out of 5
0 reviews

Podcast sponsorship advertising

Start advertising on Muhallinka Rayuwarka & sponsor relevant audience podcasts


What do you want to promote?

Ad Format

Campaign Budget

Business Details