1564127493
Madubin Usman Kabara

Advertise on podcast: Madubin Usman Kabara

Rating
★★★★★
5
from
1 reviews
This podcast has
20 episodes
Language
English
Publisher
Usman Kabara
Explicit
No
Date created
2021/04/21
Latest episode
2026/11/08
Average duration
48 min.
Release period
1 days

Description

Ina hira da kowa game da rayuwa.

Unlock Madubin Usman Kabara podcast Email contact info,
Listeners & Audience details

Email contact information

Direct podcast contact details

Listeners

Audience numbers & engagement insights

Audience details

Podcast Insights

Podcast episodes

Check latest episodes from Madubin Usman Kabara podcast


MOHAMMED LADAN | Madubin Usman Kabara #19
2026/11/08
Mohammed Ladan dai an fi saninsa da suna Dakta Ladan, sakamakon wani fitaccen shirin lafiya na gidan radiyon sashen Hausa na Muryar Amurka. Amma a likitance shi masanin kimiyyar hada magunguna ne wato ‘phamacist’. Dan asalin jihar Neja ne da ke Arewacin Najeriya, sannan a yanzu mazaunin Amurka fiye da shekara 40 tun bayan zuwansa karatu.
BELLO SISCO | Madubin Usman Kabara #18
2026/11/07
Bello haifaffen birnin Maiduguri ne amma girman Kano a tarayyar Najeriya, wanda ya ci karo da kalubalen rayuwa a dalilin basirarsa ta waka wanda har korarsa daga gidansu aka yi. Amma maimakon ya saduda, sai ma ya tsalleke kasar zuwa Jamus a tarayyar Turai inda a yanzu haka yake zaune a matsayin mawaki kuma mai koyar da rawa.
AISHA RIMI | Madubin Usman Kabara #17
2026/11/06
Aisha Rimi ‘yar kasar Birtaniya ce wacce iyaiyenta ‘yan asalin Arewacin Najeriya ne. Duk da fadawa hatsarin da ya yi sanadiyyar rabata da kafarta daya, to amma hakan bai canza komai a samun nasararta a rayuwa ba.
YUSUF AL-HASSAN | Madubin Usman Kabara #16
2026/11/05
Farfesa Yusuf Al-Hassan dan asalin cikin birnin Kano ne a Najeriya da ya kwashe shekaru yana koyo da koyarwa a tsakanin Najeriya da Amurka game da ilimin fasahar sana’o’in hannu inda har ya taba zama zakaran gasar malaman koyar da sana’o’i ta Amurka.
ALIYU MUSTAPHA | Madubin Usman Kabara #15
2026/11/04
Aliyu bakano ne a Najeriya wanda ya ke zaune a kasar Masira sannan ya shiga gasar kasidar larabci ta duniya mai taken Yariman Sha’iran Larabawa a birnin Abu Dhabi ta hadaddiyar daular larabawa. Ya tattauna damu game da rayuwarsa tsakanin Najeriya da Misira da kuma yadda aka yi ya sami shiga gasar larabawa a matsayinsa na bahaushe.
ABBA ZUBAIR | Madubin Usman Kabara #14
2026/11/03
Farfesa Abba Zubair Chedi na asibitin Mayo Clinic da ke Amurka, dan asalin jihar Kano ne a Najeriya da ya yi kaurin suna a Amurka, musamman a lokacin da ya shiga binciken yadda za a yi amfani da kimiyyar kwayar halitta ta 'stem cell' wajen kirkirar sassan jikin bil'adama, kamar zuciya da huhu don dasa wa mutanen da sassan jikin ya lalace ba tare da jiran sai wani ya mutum a cire a saka wa wani ba.
KAKA HAUWA | Madubin Usman Kabara #13
2026/11/02
Na yi hira da Hauwa Mustapha Babura da aka fi sani da Kaka Hauwa ko 'Yar Babura, 'yar asalin garin Babura ce da ke jihar Jigawa ta Arewacin Najeriya. Ta bani labarin rayuwarta tun bayan shigarta Amurka da kuruciya, inda a yanzu haka 'yar kasa ce a can kamar yadda take a kasarta ta asali. Da kuma yadda aka yi ta zama kwararriyar malamar makaranta a bangaren ilimin kananan yara da kuma yadda ake renon kwakwalwarsu.
SARATITIN BABA | Madubin Usman Kabara #12
2026/11/01
Na yi hira da kwararriyar ungozoma Saratu Garba Abdullahi wacce aka fi sani da Saratitin Baba, ‘yar jihar Jigawa ce da ke Arewacin Najeriya, shiga cikin hirar don jin yadda ta sha alwashin cika burin mahaifinta, inda ta bazama tun daga digirin farko da na biyu tsakanın Najeriya da India, har zuwa digiri na uku a Amurka.
MURTALA MAI | Madubin Usman Kabara #11
2026/10/31
Murtala Mai, likitan yara ne dan asalin jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya , da ya rikide zuwa kwararren masanin lafiyar al’umma, ya fada min yadda rayuwarsa ta kasance ta aiki har zuwa komawarsa Amurka sakamakon aikinsa na hukumar tallafi mai zaman kanta ta Pathfinder International a matsayin shugaban bangaren ayyukan Afirka.
FADJI MAINA | Madubin Usman Kabara #10
2026/10/30
Hirata da Fadji Maina 'yar kasar Nijar kuma masaniyar kimiyyar ruwa da doron kasa da ke aiki a hukumar sama-jannatin Amurka ta NASA. Tana daya daga cikin wacce mujallar tereren arziki ta Forbes ta wallafa sunanta a cikin matasa na duniya guda 30 ‘yan kasa da shekara 30 da suka sami nasara a rayuwa.
SARKI ABBA | Madubin Usman Kabara #9
2026/10/29
A shekarar 1984 a Najeriya an sami dan jihar Kano da ya fi kowane dalibi a Najeriya cin makin jarrabawar gama sakandaren kasashen Afirka ta WAEC a takaice. Yanzu haka dai wannan dalibin mai suna Sarki Abba Abdulkadir farfesa ne a bangaren haddasuwar cututtuka a Jami'ar Northwestern University da ke Chicago a Amurka.
MEEMA ESTEE | Madubin Usman Kabara #8
2026/10/28
Munira Sulaiman Tanimu (Meema Estee) na daya daga cikin zaratan matasan mata a Arewacin Najeriya wadda ta ciri tuta a bangaren tallafawa ilimin ‘ya’ya mata ‘yan talla ta hanyar jefar da Tire a rungumi Littafi.
ADAMU BAMALLI | Madubin Usman Kabara #7
2026/10/27
Adamu Hamza Bamalli ya sha gwagwarmaya a Najeriya da Amurka kama daga zama direban babbar mota zuwa rikidewa ya zama kwararren Injiniya a jihar Maryland ta Amurka. Akwai darussa matuka a tarihin rayuwar wannan jarumin.
IMRANA BUBA | Madubin Usman Kabara #6
2026/10/26
Imrana Alhaji Buba matashi ne danye shataf daga jihar Yobe, wanda har yanzu bai shekara talatin da haihuwa ba, sannan ba dan masu kudi ko mulki ba ne, amma ya sami nasararorin rayuwar da har Sarauniyar Ingila sai da ta karrama shi saboda wasu dalilan da matashin ya bayyana a wannan tattaunawa da mu ka yi dashi game da tarihin rayuwarsa.
HALIMA DJIMRAO | Madubin Usman Kabara #5
2026/10/25
Halima Djimrao tsohuwar ma’aikaciyar sashen Hausa na Muryar Amurka, ta yi doguwar hira game da rayuwarta tun daga haihuwa har zuwa girmanta da karatunta na addini dana zamani, da ma yadda aka yi ta sami aiki a Muryar Amurka da ke birnin Washington DC da kuma dalilin yin ritayarta a lokacin da duniyar aikin radiyo ke yayinta.

Podcast reviews

Read Madubin Usman Kabara podcast reviews


5 out of 5
1 reviews

Podcast sponsorship advertising

Start advertising on Madubin Usman Kabara relevant audience podcasts


What do you want to promote?