1577793201
Wasanni

Advertise on podcast: Wasanni

Categories
Country
United States
This podcast has
26 episodes
Language
English
Publisher
RFI Hausa
Explicit
No
Date created
2021/07/22
Latest episode
2026/11/02
Average duration
10 min.
Release period
9 days

Description

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Unlock Wasanni podcast Email contact info,
Listeners & Audience details

Email contact information

Direct podcast contact details

Listeners

Audience numbers & engagement insights

Audience details

Podcast Insights

Podcast episodes

Check latest episodes from Wasanni podcast


Sharhi akan kyautar Ballon d'Or ta 2026 wadda Harry Kane ya lashe
2026/11/02
Shirin 'Duniyar Wasanni' tare da Khamis Saleh zai maida hankali ne kan kyautar Ballon d’Or da aka bayar a ranar Litinin ɗin data gabata. Kyaftin ɗin tawagar Ingila Harry Kane ya lashe kyautar a bana, inda ya zamo ɗan wasan ƙasar na farko daya lashe ta cikin shekaru 25, wato tun bayan Michael Owen a shekarar 2001. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin...........
Sharhi kan yadda ta kaya a wasan El-Clasico da aka yi a ƙarshen mako
2026/10/26
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako ya maida hankali kan wasan El-Clasico da aka yi tsakanin Barcelona da Real Madrid. Shi dai wasa tsakanin waɗannan ƙungiyoyi ba wai wasa bane na gama gari, domin yanada ɗinbin tarihi ganin cewa an faro shine a shekarar 1902, kuma wancan lokacin Barcelona ce ta fara samun nasara kan Madrid da ci 3-1. Sai dai a wasan na daren jiya Lahadi Madrid ce ta samu nasara da ci 2-1. Sakamakon wannan wasa ya bada mamaki matuƙa, domin dai an yi tunanin Barcelona za ta yi wa Madrid Kukkunge ne, kasancewar tana gida tare da goyon bayan mutane dubu 62,650 da suka taru a filin wasan Spotify Camp Nou, domin ganin yadda zata kaya. Haka nan ƙungiyar ta kwashe sama da shekara guda ba tare da tayi rashin nasara a filin ba, domin rashin nasara ta ƙarshe da tayi a nan ita ce a hannun Villarreal a ranar 18 ga watan Mayun shekarar bara, gashi kuma tayi nasara a wasanni 6 cikin 7 na haɗuwarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............
Nasarar tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya akan Comoros
2026/10/19
Shirin 'Duniya Wasanni' a wanan mako tare da Khamis Saleh zai dubu ne kan nasarar da tawagar Super Falcons ta samu kan Comoros, inda a makon da ya gabata ne aka kammala wasa na biyu na zagaye na biyu na neman zuwa gasar Olympics da aka yi tsakanin tawagar mata ta Super Falcons ta Najeriya da takwararta ta Coromos. An dai buga dukkanin wasanni biyu ne a filin wasa na Remon Star da ke garin Ikenne na jihar Ogun, inda a wasan farko Super Falcons ta samu nasara da ci 2 da nemam sannan a wasa na biyu aka tashi 5 da nema, a jumlace gida da waje Najeriya ta jefa kwallaye biyar da nema a ragar Comoros.
Messi ya yi bankwana da tawagar Argentina bayan doka wasanni 208
2026/10/12
Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan mako, zai dubu ne kan bankwanan da Lionel Messi ya yi da tawagar Argentina. A farkon watan Oktoban nan da muke ciki ne kyaftin ɗin tawagar ƙasar Argentina Lionel Messi, yayi bankwana da tawagar bayan kwashe tsawon shekaru 21 tana wakiltar ƙasar a wasannin matakin ƙasa da ƙasa. Messi ya fara bugawa Argentina wasanni ne a ranar 17 ga watan Agustan shekarar 2005 a wani wasan sada zumunci da suka yi da Hungry, inda ya samu nasarar buga wasanni 208, kafin murabus ɗinsa a ƙarawarsu da Benin a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2026. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..
Yadda ƴan wasa ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin hutu
2026/10/05
Shirin a wannan mako ya yi duba ne kan yadda ƴan wasan da ke taka leda ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin da suke hutu. A duk lokacin da aka kammala wasannin lig-lig a kan tafi hutu a kowace shekara musamman a nahiyar Turai da lig ɗin su ya fi jan hankali, wanda hakan kuma ke buɗe wani babi na wasanni a yankuna daban-daban da ƴan wasan ke fitowa domin nuna bajintarsu a zahiri a wasannin sada zumunta da a ke shirya musu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
An kammala gasar tseren Keke ta ƙasa karo na 6 a Jamhuriyyar Nijar
2026/09/28
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda aka gudanar da gasar tseren keke a jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar. Wannan ne dai karo na 6 da ake gudanar da gasar da ta haɗa masu wannan wasa daga jihohi 8 na ƙasar, da nufin samun gwarazan shekara sannan kuma a zaɓa ƴan wasan da za su rinƙa wakiltar ƙasar a gasanni daban daban kama daga nahiyar Afirka dama matakin duniya idan dama ta samu. Ku latsa alamar sauto don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............
Duniyar Wasanni: Wace waina ake toyawa a gasar Frimiya Lig ta Ingila
2026/09/21
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda al’amura ke gudana a gasar Firimiya lig ta Ingila. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh
Ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a matakin Unguwanni sun fara cinikayyar ƴan wasa
2026/09/07
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda ake cinikayyar ƴan wasa a matakin ƙananan ƙungiyoyin Unguwanni. A yanzu dai ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke buga wasanni a matakin Unguwanni a jihar Kaduna, tuni suka rungumi tsarin cinikayyar ƴan wasa domin ƙarawa ƙungiyoyinsu ƙarfi. Wasu daga cikin masu horas da irin waɗannan ƙungiyoyi sun ce wannan tsarin cinikayya ya taimaka wajen kawo ƙarshen rigingimu da a ke samu kan ƴan wasa, sannan kuma ana gudanar da ita ne kan kuɗin da suka fara daga naira dubu 30 zuwa sama. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
Shugabanni hukumar NFF sun yi murabus bayan kiraye-kirayen ƴan Najeriya
2026/08/31
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan murabus ɗin da shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya NFF Alhaji Ibrahim Gusau da wasu daga cikin mambobin kwamitin zartarwarsa suka yi, bayan matsin lambar da suka fuskanta kan koma bayan da tawagogin ƙasar suka samu a manyan gasanni na duniya, ciki har da gaza samun gurbin da tawagar mata ta ƙasar ta yi a gasar lashe kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa. A cewar rahotanni, 8 daga cikin mambobin kwamitin 13 ne suka yi murabus daga jagorancin hukumar ta NFF, lamarin da ya haifar da shakku gameda zaɓen shugabannin hukumar da za a yi nan ba da jimaba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............
An fara yunƙurin rushe kwamitin ƙoli na hukumar NFF a Najeriya
2026/08/24
Shirin Duniyar Wasanni na yau ya mayar da hankali kan dambarwar da ta kunno kai a sashen wasanni na Najeriya bayan da hukumar wasannin ƙasar ta baiwa mambobin kwamitin ƙolin NFF wa’adin sa’o’i 24 tun a juma’ar da ta gabata kan su ajje aiki. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Manyan kalubalen da tawagogin ƙwallon ƙafar Najeriya ke fuskanta a harakar wasanni
2026/08/17
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya yi duba ne kan irin koma bayan da ake gani na faruwa a tsakanin tawagogin kwallon kafar Najeriya, kama daga bangaren mata mata da maza, har ma da yan wasa masu tasowa. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Yadda ba a samun sabbin ƙasashen da ke lashe Gasar Kofin Duniya
2026/07/27
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda ba a samun sabbin ƙasashen da ke lashe gasar kofin duniya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Spain ta lashe kofin duniya karo na biyu a tarihi
2026/07/20
Shirin Duniyar wasanni a wannan makon tare da Khamis Saleh ya yi duba ne a gameda  nasarar da tawagar Spain ta yi kan takwararta ta Argentina a gasar cin kofin duniya karo na 23 Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Sharhin yadda wasannin kwata final na gasar cin kofin duniya suka gudana
2026/07/13
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan wasannin gab da na kusa da ƙarshe na gasar cin kofin duniya da aka kammala tsakanin ƙasashe 8 wanda kuma kawo yanzu ya rage ƙasashe 4 a wannan tafiya wadda ta faro da ƙasashe 48. A wasannin dai Faransa ta yi waje da Morocco yayinda Spain ta yi waje da Belgium kana Ingila ta yi waje da Norway yayinda Argentina mai kare kambun gasar ta yi waje da Switzerland. Hankula sun karkata ga wasannin ƴan huɗu da suka rage a wannan gasa don ganin waɗanda zasu kai wasan ƙarshe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....
Tawagogin ƙasashen Afirka 7da aka yi waje dasu bayan sun tsallaka zagayen ƴan 32
2026/07/06
Bayan nasarar da tawagogin ƙasashen Afrika 9 suka yi na kaiwa zagayen ƴan 32 a gasar lashe kofin duniya, wani lamari da ya sanya nahiyar ta kafa tarihin samun yawan wakilai a wannan zagaye, sai dai kuma ana iya cewa murna ta koma ciki domin dai tuni aka yi waje da 7 daga cikin 9. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........

Podcast reviews

Read Wasanni podcast reviews


0 out of 5
0 reviews

Podcast sponsorship advertising

Start advertising on Wasanni relevant audience podcasts


What do you want to promote?