Mu Zagaya Duniya

Advertise on podcast: Mu Zagaya Duniya

Categories
This podcast has
31 episodes
Language
Publisher
Explicit
No
Date created
2015/07/07
Latest episode
2026/04/18
Average duration
21 min.
Release period
9 days

Description

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

Unlock Mu Zagaya Duniya podcast Email contact info,
Listeners & Audience details

Email contact information

Direct podcast contact details

Listeners

Audience numbers & engagement insights

Audience details

Podcast Insights

Social media

Check Mu Zagaya Duniya social media presence


Podcast episodes

Check latest episodes from Mu Zagaya Duniya podcast


Makomar masu shiga tsakani,kan neman ƙulla yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran
2026/04/18
Mecece makomar ƙoƙari da masu shiga tsakanin, musamman Pakistan ke yi a kan neman ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran duba da tsaurin wasu ko da dama daga cikin sharuɗɗan da ɓangarorin biyu suka gabatarwa juna? Nura Ado Suleiman ke  yi muku barka da sake haɗuwa cikin shirin Duniyarmu a Yau
more
Bitar Labaran mako: Iran ta amince da buɗe mashigin Hormuz ga jiragen kasuwanci
2026/04/18
Shirin Mu zagaya duniya tare da Oumarou Sani, kamar yadda ya ke zuwar muku a kowannen mako, a wannan karon ma ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke ban kwana da shi. Cikin jerin labaran da ke ƙunshe a wannan shiri, akwai yadda Iran ta amince da buɗe mashigin Hormuz bayan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 10 tsakanin Isra'ila da Lebanon. Wannan da sauran manyan labarai daga sassa daban-daban na nan ƙunshe a cikin shirin. Ku latsa alamar sauti don saurare.
more
An cimma yarjejeniyar tsagaita wutar makwanni 2 tsakanin Amurka da Iran
2026/04/11
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Oumaru Sani, ya yi bitar wasu daga cikin muhimman labaru kan lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana, daga cikinsu kuma akwai yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 14 da aka cimma tsakanin Amurka da Iran, bayan da ƙasar Pakistan ta shiga tsakani.
more
Rikicin Gabas ta Tsakkiya: Dakarun Amurka sama da 2000 sun isa yankin
2026/04/04
Shirin mu na yau ya fara yadda zango a yankin Gabas ta Tsakiya inda rikicin Amurka da Isra’ila kan Iran ke cigaba da tsananta duk da tayin shiga tsakani da wasu kasashen Larabawa su ka faro karshen mako a Pakistan  da zummar kawo karshen rikicin da tuni ya kasara tattalin arzikin duniya. A cikin ranakun ƙarshen mako kamfanin dilancin labaran Reuters ya bayyana cewa sojojin Amurkan dubu 2 da 500 sun isa yankin na Gabas ta Tsakiya. 
more
Wane hali ake ciki game da yaƙin Gabas ta tsakiya
2026/03/28
Shirin Mu zagaya Duniya na wannan rana ya mayar da hankali kan yakin Gabas ta tsakiya da halin da yanayin tsaro ke ciki a Najeriya da sauran manyan labaran da suka faru a sassan duniya cikin wannan mako. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sanni.
more
Yadda rikicin Iran ke faɗaɗa a yankin Gabas ta Tsakiya
2026/03/07
A Wanan makon shirin zai karkata alakarsa ne yankin Gabas ta Tsakiya inda sabon rikici ya barke tsakanin hadakar Amurka da Isra’ila da kuma Iran. A cikin shirin zamu yi duba dangane da yadda rikicin  ke cigaba da faɗaɗa zuwa sauran kasashen yankin da ma  tasirinsa kan bangarori daban-daban a  wanan duniyar sai a gyara zama domin sauraron cikakakken shirin.
more
Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci Pakistan da Afghanistan su kai zuciya nesa
2026/02/28
Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Oumarou Sani ya mayar da hankali kan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka bankwana da shi, masamman kan ƙazancewar rikici tsakanin Afghanistan da Pakistan, bayan da Pakistan ta ƙaddamar da harin Operation Ghazab lil-Haq a matsayin martani ga hare-haren da tace Taliban ta kai wa sojojinta, da kuma dambarwar Amurka da Iran kan yarjejeniyar ƙera makaman nukiliya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiin tare Oumarou Sani...............
more
Sanya hannu kan dokar zaɓe da Tinubu ya yi ta bar baya da ƙura
2026/02/21
Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Oumarou Sani kamar ya mayar da hankali kan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka bankwana da shi, masamman kan dambarwar da ta biyo bayan sa hannun da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yiwa dokar zaɓen ƙasar, da kuma mummunar gobarar da aka samu a kasuwar Singa da ke jihar Kano. Haka nan shirin ya yi bitar hukuncin ɗaurin rai da rai da Kotu a Korea ta Kudu, ta yankewa tsohon shugaban ƙasar Yoon Suk-Yeol. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiin tare Oumarou Sani...............
more
Harin Kwara da dambarwar Nukiliyar Iran na cikin manyan labaran makon da ya gabata
2026/02/07
Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Oumar Sani kamar kullum ya mayar da hankali kan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka bankwana da shi, masamman harin da ya kashe sama da mutane 170 a jihar Kwara dake arewacin Najeriya. 
more
Ƙungiyar IS ta dau alhakin harin da aka kai filin tashin da saukar jirage na Diori Hamani a Nijar
2026/01/31
A daren Laraba zuwa wayewar ranar Alhamis, filin jirgin saman Diori Hamani na Yamai da ke jamhuriyar Nijar ya fuskanci wani hari na ɗan lokaci daga wasu mayaka na ƙungiyar IS. Gwamnatin sojin Nijar, tare da taimakon sojojin Rasha,ta murkushe maharan. A yanzu haka,jiragen sama sun ci gaba da zirga-zirga, a cewar hukumar da ke kula da harkokin sufurin jiragen sama na ƙasar.
more
Kisan mutane 7 ƴan gida ɗaya ya tayar da hankalin jama'a a Kano
2026/01/25
Daga cikin abubuwan da Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan  mako ya yi duba akai har da batun kisan Fatima Abubakar da ƴaƴanta 6 a Unguwar Ɗorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin......
more
Aƙalla mutane 5000 ake fargabar sun mutu a zanga-zangar Iran
2026/01/17
Mahukuntan Iran sun yi barzanar amfani da hukuncin kisa kan masu zanga-zangar wadda ta juye zuwa tarzoma inda ofishin babban mai shigar da ƙara na gwamnati ya ce akwai yiwuwar idan aka fara ɗaukar wannan mataki a samu sassaucin zanga-zangar. A nasa bangare shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar mataki mai tsauri kan Iran muddun hukumomin ƙasar suka fara kashe masu  zanga-zangar tsadar rayuwa.
more
Bitar muhimman labaran da suka gudana a makon da muke bankwana da shi
2026/01/10
A cikin shirin na wannan mako tare da Oumarou Sani, zakuji bitar muhimman labaran da suka wakana a makon da muke bakwana da shi, ciki har da yadda Amurka ta yi gaban kanta wajen kutsawa cikin Venezuela tare da kame shugaba Nicolas Maduro. Muna tafe da tattaunawar masana a ɓangarori daban-daban kan wannan katsalandan na Amurka. Hallau dai a cikin shirin zaku ji bitar ɓarkewar sabon rikici a Yemen da Syria. A Najeriya kuwa akwai mu da bitar hare-haren ƴan ta'adda a jihar Neja da kuma rikicin siyasar ƙasar. Ku latsa lamar sauti don sauraron cikakken shirin.
more
Sabuwar dokar haraji ta shafi rayuwar ‘yan Najeriya - tattalin arziki
2026/01/03
Sabon shirin  Mu Zagaya Duniya wanda ke bitar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana daga nan sashen hausa na Rfi.
Najeriya ta tabbatar da harin da Amurka ta kai a wasu yankuna na jihar Sokoto
2025/12/27
A cikin daren  ranar Alhamis da ta gabata Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da harin da Amurka ta kai a wasu yankuna biyu na jihar Sokoto wato Tangaza inda nan ne ‘yan Lakurawa ke da maɓoya da kuma Jabo da ke yankin ƙaramar hukumar Tambuwal. Sai dai mazauna yankin Jabo sun bayyana fargabar zama a ƙauyukansu saboda fargabar yin kuskuren kai musu farmaki a yayin wasu hare-haren da watakila Amurkar ka iya kai wa a nan gaba.
more

Podcast reviews

Read Mu Zagaya Duniya podcast reviews


0 out of 5
0 reviews

Podcast sponsorship advertising

Start advertising on Mu Zagaya Duniya & sponsor relevant audience podcasts


What do you want to promote?

Ad Format

Campaign Budget

Business Details