
Advertise on podcast: Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
This podcast has
25 episodes
Language
EnglishPublisher
RFI HausaExplicit
No
Date created
2021/07/22
Latest episode
2026/02/03
Average duration
10 min.
Release period
5 days
Description
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…
Unlock Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare podcast Email contact info,
Listeners & Audience details
Email contact information
Direct podcast contact details

Listeners
Audience numbers & engagement insights

Audience details
Podcast Insights

Podcast episodes
Check latest episodes from Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare podcast
Ra'ayoyin masu sauraro kan kyautar Grammy da Fela Kuti ya samu bayan rasuwarsa
2026/02/03
Shekaru 29 bayan mutuwarsa, an bai wa shahararren mawaƙi kuma mai fafutuka Fela Kuti ya kasance ba’Afirke na farko da aka bai wa kyautar yabo ta Grammy wato Lifetime Achievement Award da ake bai wa wanda ya sadaukar da rayuwarsa yana rera waƙa.
Fela ɗan Najeriya, ya yi fice ainun, ta hanyar rera waƙoƙin gwagwarmaya da kuma muradun talakawa.
Shin ko me za ku iya tunawa a game Fela Kuti?
Me za ku ce a game da wannan kyauta ta Grammy Awarda aka bayar bayan rasuwarsa?
Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabambanta
2026/01/16
Yau juma'a, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tattalin arziƙin, siyasa, zamantakewa da dai sauransu.
Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabambanta...
Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda wasan kusa da na ƙarshe ya gudana a AFCON
2026/01/15
Morocco da Senegal sun yi nasarar kaiwa wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika ko kuma AFCON, nasarar da suka samu bayan ita mai masaukin baƙi ta doke Najeriya yayinda Senegal kuma ta doke Masar dukkaninsu a daren jiya Laraba, yayinda ake shirin haɗuwa don doka wasan ƙarshe na gasar tsakanin manyan ƙasashen 2 a ranar Lahadi.
Anya kuwa ƙasashen na Masar da Najeriya sun taka rawar da ta dace gabanin fitar da su daga gasar?
Wacce ƙasa kuke ganin za ta kai tsakanin labari wajen lashe kofin a wannan karon?
Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin....
Ra'ayoyin masu sauraro kan kayan aikin soji da Amurka ta bai wa Najeriya
2026/01/14
Amurka ta sanar wa bai wa Najeriya wasu muhimman kayan aikin soji domin tunkarar ƙalubale na tsaro da ƙasar ke fama da shi.
Rundunar Amurka mai kula da nahiyar Afirka wato Africom ce ta sanar da hakan, sama da makonni biyu da Amurka ta ƙaddamar da farmakin farko kan wasu wurare ta bayyana cewa maɓoyar yan ta’addace.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Yadda ɗalibai a wasu yankunan arewacin Najeriya ke zaune a gida saboda rashin tsaro
2026/01/12
A Najeriya, an koma makaranta bayan kammala hutun ƙarshen shekara, to sai dai yanzu haka akwai ɗimbin yara da ba sa zuwa makaranta saboda matsalar tsaro Mafi yawansu a jihohin Katsina, Neja, Sokoto, Zamfara da dai sauransu.
Shin ko meye makomar yaran da ba sa samun damar zuwa makaranta sakamakon wannan matsala ta tsaro?
Shin waɗannan matakai suku kamata a ɗauka don tunkarar wannan matsala da ke hana ɗimbin yara damar samun ilimi a wasu sassan Najeriya?
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Faruk Yabo.
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
2026/01/09
Yau juma'a ce ranar da sashen Hausa na RFI ta cikin shirin Ra'ayoyinku masu sauraro ke baku damar bayyana abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga sha'anin siyasa, tattalin arziƙi, zamantakewa da dai sauransu.
Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙasashe 8 da za su fafata a Quarter Finals na AFCON
2026/01/08
A gasar neman kofin Afirka da ke gudana a Morocco, a yanzu dai an tantance ƙasashe 8 da za su fafata da juna a matakin da ake kira Quarter Finals, inda Mali-Sénégal, Masar ta haɗu da Côte d'Ivoire, Kamaru ita da Morocco sai kuma Nigeria da za ta kece reni da Algéria.
Waɗannan ƙasashe 8, tun farko su ne ake hasashen cewa za su iya taka gagarumar rawa a gasar.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan miliyoyin ƴan Najeriya da basa amfani da wutar mita
2026/01/07
Hukumar daidaita farashin wutar lantarki a Najeriya ta ce yanzu haka akwai sama da layuka milyan biyar da jama’a ke amfani da wuta ba tare da an ɗora su a kan mita ba.
Wannan ya zo ne daidai lokacin da ake ci gaba da ɗiga ayar tambaya dangane da dalilan da suka sa aka gaza samar da mitocin a wadace.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan dokar harajin Najeriya da za ta fara aiki gobe
2025/12/31
A Najeriya, gobe alhamis 1 ga watan Janairu, za a fara aiwatar da sabuwar dokar haraji ta ƙasa, a cikin yanayi da dokar ke shan suka saboda dalilai da dama.
Yayin da jama’a ke cewa sabon tsarin karɓar haraji na matsayin ƙarin nauyi ne ga al’umma, hakazalika wasu ƴan majalisa sun yi zargin cewa abin da suka amince da shi ya sha bambam da abin da gwamnati ke shirin aiwatarwa.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan dokar-ta-baci da gwamnati ta kafa a Nijar
2025/12/30
Mahukuntan jamhuriyar Nijar sun shelanta kafa dokar-ta-ɓaci, wanda a ƙarƙashinta gwamnati za ta iya yin amfani da illahirin al’ummar ƙasar da kuma dukiyoyinsu duk lokacin da ta ga ya dace saboda tunkarar barazanar tsaro.
Matakin ya zo ne kwanaki ɗaya bayan da Amurka ta ƙaddamar da farmaki kan maɓoyar ƴanbindiga a wani wuri da ke jihar Sokoton Najeriya daf da iyaka da Nijar.
Shin ko me za ku ce a game da matakin?
Anya hakan zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fama da su?
Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu saurare kan harin Amurka a Najeriya
2025/12/29
Gwamnatin Najeriya ta ce da saninta Amurka ta ƙaddamar da hari jihar Sokoto da ke shiyar Arewa maso Yammacin ƙasar a makon daya gabata, inda ta ce an kai harin ne kan ƴan ta’addan da ta ce ke kwarara cikin ƙasar daga yankin Sahel.
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabir Muhammad Ɗan Bauchi.
Ra'ayoyin masu saurare kan bikin Kirismeti na bana
2025/12/25
Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda al'ummar Kirista suka gudanar da bikin Kirismeti na wannan shekara.
Ku danna alamar saurare domin sauraren shirin tare da Abdullahi Isa.
Ra'ayoyin masu saurare kan sabuwar dokar harajin Najeriya
2025/12/23
Duk da cewa mafi yawan jama’a basu da cikakkiyar masaniya ko kuma fahimta a game da sabuwar dokar haraji da gwmanatin Tinubu za ta fara aiwatarwa daga ranar 1 ga watan janairu mai zuwa amma mafi yawan jama’a na nuna fargaba dangane da wannan doka.
Wasu dai na kallon dokar a matsayin sabuwar hanya domin tatsar kuɗaɗe daga jama’a ba wai ba wai attajirai kawai ba harma daga talakawa, a daidai lokacin da wasu ke ganin gwamnati ta sauya dokar daga asalin wacce aka amince da ita.
Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
Ra'ayoyin ku masu sauraro na ranar Juma'a
2025/12/19
Yau juma ace ranar da muke baku damar tofa albarkacin bakinku kan amuran dake ci muku tuwo a kwarya wadanda suka hada da siyasa, tattalin arziki, fasaha da dai sauransu.
muna dakon ra'ayoyinku.
Sai ku latsa alamar sauti domin sauraron shirin
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta
2025/11/28
Kamar yadda aka saba a kowace ranar Juma'a, sashen Hausa na RFI na bai wa masu sauraro damar faɗin albarkacin bakinsu kan baututuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tattalin arziƙi, siyasa, zamantakewa da dai sauransu.
A yau ma mun baku wannan dama, kamar yadda za ku ji ra'ayoyi mabanbanta idan kuka latsa alamar sauti....
Podcast reviews
Read Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare podcast reviews
Podcast sponsorship advertising
Start advertising on Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare relevant audience podcasts
You may also like to advertise on these Podcasts

4.4371061566
The Megyn Kelly Show
SiriusXM

4.888901269
Fearless with Jason Whitlock
Blaze Podcast Network

4.8118931000
Mind Pump: Raw Fitness Truth
Sal Di Stefano, Adam Schafer, Justin Andrews, Doug Egge

4.8102131585
Tara Brach
Tara Brach

4.541561215
Something You Should Know
Mike Carruthers | OmniCast Media

4.513841343
Strictly Anonymous Confessions
Kathy Kay

4.8292781897
Fantasy Footballers - Fantasy Football Podcast
Fantasy Football

4.62382612
Football Weekly
The Guardian

4.45387666
Two Judgey Girls
Two Judgey Girls

3.8258501152
The Viall Files
Nick Viall